Da Dumi Dumi

Coronavirus: Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya ya killace kansa

Gwamnan jihar Ekiti Dakta Kayode Fayemi, kuma shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya ya killace kansa a daidai lokacin da ake jiran sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar coronavirus.

Gwamnan ya bada sanarwar hakan ne a shafinsa na Twitter cewa, tun a ranar Talata ya killace kansa bayan ta tabbata cewa ya yi mu’amala da wasu mutum biyu da suka kamu da cutar Coronavirus.

Ko da yake gwamnan bai fadi sunan mutum biyu da ya ce, ya yi mu’amalar da su ba, ana kyautata zaton mutum biyun da yake nufi sun hada da: Shugaban ma’akatan gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi Muhammad Bala Abdulkadir wanda a baya bayan nan suka kamu da cutar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya