Da Dumi Dumi

Coronavirus: Kasuwannin da Gwamnatin Legas ta rufe

Daya daga cikin Kasuwannin Legas

Ranar Alhamis ne umarnin da Gwamnatin Jihar Legas ta bayar na rufe kasuwanni zai fara aiki a matsayin matakin da ake ci gaba da dauka domin hana yaduwar cutar Coronavirus.

A cikin makon nan ne gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umarnin rufe wasu kasuwannin jihar ban da kasuwannin da ake sayar da kayan abinci da magunguna ko ruwan sha.

Kasuwannin da umarnin na gwamnatin Legas ya shafa su ne:

 1. Babbar kasuwar sayar da wayoyin salula da dangoginta ta Computer Village da ke Ikeja wato kasuwar GSM village.
 2. Kasuwar Mandilaz da ke cikin garin Legas

3. Kasuwar Oluwale da ke cikin garin Legas

 1. Kasuwar Ogba
 2. Kasuwar Ladipo da ake sayar da kayan motoci
 3. Kasuwar Arena da ke Oshodi
 4. Daukacin Kasuwar Oshodi
 5. Kasuwar Lawason
 6. Kasuwar Gatankowa
 7. Kasuwar kayan lantarki ta duniya da ke Alaba wato Alaba International Market
 8. Kasuwar Baje Koli wato Trade Fair Market
 9. Kasuwar Igando da Alimosho, da ta Abule-egba
 10. Kasuwar Ebute Ero
 11. Kasuwar Computer Village da ke Ikeja
 12. Kasuwar Balogun da ke cikin birnin Lagos
 13. Kasuwar Iyana-Ipaja
 14. Kasuwar Agege

Gwaamnatin ta bayar da umarnin rufe wadannan kasuwanni ne domin rage cunkoson jama’a a birnin Legas.

ADVERTISEMENT

Jihar Legas ita ce jihar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

Kasuwar Legas

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya