✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kashe dan jarida a Zimbabiwe

Wani dan jarida ya zama mutum na farko da ya mutu a kasar Zimbabiwe bayan ya kamu da cutar Coronavirus. Ministan kiwon lafiya na kasar,…

Wani dan jarida ya zama mutum na farko da ya mutu a kasar Zimbabiwe bayan ya kamu da cutar Coronavirus.

Ministan kiwon lafiya na kasar, Obadiah Moyo, ne ya tabbatar da hakan, yana cewa mutumin mai shekara 30 sunansa Zororo Makamba.

Ya ce dan jaridar ya rasu ne a Asibitin Wilkins da ke birnin Harare kwanaki biyu bayan kwantar da shi a asibitin a sakamakon cutar Coronavirus.

A nata bangaren Ministar Yada Labarai ta kasar, Monica Mutsvangwa ta bayyana alhininta game da mutuwar dan jarida Zororo tana cewa ya dawo gidansa a ranar 9 ga watan Maris daga Birnin New York na kasar Amurka, inda ya fara nuna alamun ciwon murar mashako.

“Bayan an kwantar da shi ya ci gaba da nuna alamun sarkewar numfashi inda aka killace shi, zuwa yanzu ana neman mutanen da ya yi mu’amala da su domin a killace su,” In ji Mutsvangwa.

Ta ce a daidai lokacin da suke alhinin mutuwar Zororo zai yi kyau jama’a su ci gaba da daukar matakan kariya daga cutar COVID-19, kana su dauke ta da mahimmanci kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ke fadakarwa.

A Najeriya ma a ranar Litinin da ta gabata ne mutum na farko da ya kamu da cutar ya mutu a asibitin da aka killace shi a Abuja, mutumin mai suna Suleiman Achimugu tsohon Darakta ne a Hukumar Kayyade Farashin Man fetur, wato PPMC.