✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: ’Yan Najeriya uku sun mutu a Amurka

Babban Jami’i mai kula da karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin New York na Amurka, Benaoyagha Okoyen, ya tabbatar da mutuwar mutum uku ’yan…

Babban Jami’i mai kula da karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin New York na Amurka, Benaoyagha Okoyen, ya tabbatar da mutuwar mutum uku ’yan Najeriya sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus.

Daga cikin wadanda suka rasu akwai wani likita daga jihar Abiya wanda cutar ta yi ajalinsa lokacin da yake bakin aiki a wata cibiyar hana yaduwar cutar a birnin na New York.

Sai na biyun kuma wani matashi ne mai shekara 25 mai suna Bassey Offiong, wanda yake shekarar karshe ta karatun digiri a Jami’an Yammacin Michigan.

Sai kuma wata mata mai suna Hajiya Laila Abubakar Ali, ’yar asalin jihar Kano, mai shekara 60.

Ta rasu ne a ranar 25 ga watan Maris a Asibitin Lincoln da ke yankin Bronx, a jihar New York.