✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An kafa dokar hana fita a Daura

Sanadiyar bullar cutar coronavirus a Daura ta hanyar mutuwar wani likita, gwamnatin jihar Katsina ta rufe duk iyakokin karamar hukumar Daura tun daga gobe Asabar…

Sanadiyar bullar cutar coronavirus a Daura ta hanyar mutuwar wani likita, gwamnatin jihar Katsina ta rufe duk iyakokin karamar hukumar Daura tun daga gobe Asabar da karfe 7:00 na safe har sai abin da hali ya yi.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, ne ya shaidawa manema labarai hakan, cewa bayan rasuwar Dokta Aliyu an samu mutum 23 da suka yi mu’amulla da shi wadanda aka debi jininsu domin gwaji.

Daga cikin mutanen an samu mutum uku masu dauke da cutar coronavirus, matar shi da yaran shi biyu.

Samuwar hakan yasa, kwamitin ko ta kwana akan cutar gami da jami’an kiwon lafiya da na tsaro suka yi taron gaugawa inda aka yanke hukuncin rufe garin Daura da wasu yankunan da ke kusa da ita tare kuma ci gaba da binciko wadanda suka yi alaqa da shi mamacin domin ci gaba da bincikensu don ganin an dakile yaduwar wannan cuta a duk fadin jihar.

“Wannan rufe karamar hukumar, an yi ne domin bayar da dama ga masu bukatar sayen wani abu zasu samu dama. Sannan rufewar bata shafi kantunan sayar da magani da masu sayar da abinci ba.

A cewar Gwamnan, tuni an dauko su wadannan mutane uku zuwa asibitin kwararru da ke cikin garin Katsina a inda ake killace masu wannan cutar.

Gwamnan ya kara da cewa, duk wata karamar hukumar da aka samu da wannan matsalar za’a rufe ta. Sannan ya bukaci jama’ar Daura su kiyaye doka, kowa ya zauna a gida har sai wata larura mai karfi.