✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An sake rufe makarantu a Amurka

Hukumomi a birnin New York sun ba da umarnin rufe makarantu a ranar Laraba, bayan samun karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 kwanaki…

Hukumomi a birnin New York sun ba da umarnin rufe makarantu a ranar Laraba, bayan samun karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 kwanaki bakwai a jere.

A karshen watan Satumba zuwa farkon watan Oktoba yara suka koma Makaranta lokacin da yawan masu kamuwa da cutar ke kasa da kashi biyu cikin 100.

Ranar Laraba, Karamar Hukumar Clark da ke jihar Nevada, wadda ta hada da birnin Las Vegas, ta kaddamar da wata manhajar waya da ake kira “FixIt,” wadda da ita mazauna za su iya bayar da rahoto kan batutuwa da suka hada da saba wa dokar coronavirus.

A ranar Talata, garin New Orleans ya sanar cewa zai soke jerin gwanon bikin Mardi Gras a watan Fabrairu, saboda karuar cutar coronavirus a yawancin yankunan Amurka.

A jihar California kuma, birnin Los Angeles ya umarci gidajen cin abinci da na sayar da barasa masu budaddun wuraren ajiye mutane, da su rage adadin kwastomominsu zuwa kashi 50%, su kuma su rika rufe wuraren da misalin karfe 10 na dare.

Rufaffun wurare kuma, kamar shagunan marasa mahimmanci sosai su rage adadin mutanen da suke samu zuwa kashi 25% cikin 100%.

Ana daukar dukkan wadannan matakan ne domin magance sake yaduwar cutar a tsakanin al’umar kasar.