✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Saudiyya za ta biya iyalan ma’ikatan da suka mutu diyya

Saudiyya za ta ba wa iyalan likitocin da suka mutu a bakin aikin kula da masu fama da cutar COVID-19 a kasarta. Gwamnatin Saudiya ta…

Saudiyya za ta ba wa iyalan likitocin da suka mutu a bakin aikin kula da masu fama da cutar COVID-19 a kasarta.

Gwamnatin Saudiya ta amince a biya diyyar Riyal 500,000, kimanin Naira miliyan 61, ga ilayan kowanne daga likitocin.

Iyalan likitoci akalla goma ne za su karbi diyyar kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a ranar Talata.

Sanarwar ta ce za a ba da diyyar ce kan likitocin asibitocin gwamnati da masu zaman Kansu, ‘yan asalin Saudiya da ma ‘yan kasashen waje.

Ta ci gaba da cewa za kuma a bayar da irinsa kan ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro da na farin kaya da annobar ta yi ajalinsu a bakin aikinsu.

Ta ce wadanda za a biya diyyarsu su ne wadanda aka sanar da gwamnati a hukumance cewa sun rasa rayukansu a bakin aiki.

Sanarwar ta yi bayani cewa gwamnatin kasar ta samu rahotan jami’an lafiya na farko da ya rasu a annobar a ranar 31 ga watan Maris, 2020.