Da Dumi Dumi

Cutar Korona: Najeriya ta dage Bikin Wasanni na Kasa Edo 2020

Sunday Dare yayin da yake wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayanin kan Edo 2020.
Sunday Dare yayin da yake wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayanin kan Edo 2020.

An dage Bikin Wasanni na Kasa karo na 20 da aka shirya za a fara a karshen makon nan a Jihar Edo. Ministan Matasa da Wasanni Sunday Dare ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter a ranar Talata.  Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Wasanni ta Tarayya ta yi wata ganawa da takwararta Ma’akatar Lafiya, kuma ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage duk wani wasa da ake yi na shekara har sai abin da hali ya yi.

Ga abin da ya rubuta: “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a dage Bikin  Wasanni na Kasa, wato Edo 2020 saboda daukar matakan kariya a kan yada cutar Kurona (COBID-19).

“Bayan ni da Minista a Ma’aikatar Lafiya mun yi masa bayani, kan COBID 19, Shugaban Kasa ya amince a dage Bikin Wasannin na Edo zuwa nan gaba.”

Kafin wannan sanarwa jama’a da dama sun yi ta kira a dage wannan gasa saboda tsoron yaduwar cutar Kurona.

Kamar yadda masu shirya gasar suka sanar ana sa ran ’yan wasa kimanin dubu 11 tare da masu horar da su za su halarci wannan gasa ta Edo 2020.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya