✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: China ta fadada matakan takaita zirga-zirga

Mahukuntan kasar China sun sanar da kara takaita zirga-zirgar jama’a a kusa da birnin Shanghai cibiyar kasuwanci ta kasar a wani yunkuri na hana yaduwar…

Mahukuntan kasar China sun sanar da kara takaita zirga-zirgar jama’a a kusa da birnin Shanghai cibiyar kasuwanci ta kasar a wani yunkuri na hana yaduwar cutar Kurona bayan da a karon farko ta hallaka mutum daya a Hong-Kong.

A watan Janairun da ya gabata ne mutumin dan shekara 39 da ke fama da rashin lafiya ya kai ziyara birnin Wuhan na China inda a can ne cutar ta Coronabirus ta bayyana a watan Disamban da ya gabata.

Domin hana yaduwar cutar yankin Hong-Kong ya dauki matakin rufe illahirin iyakokin kasa ban da wasu gadoji biyu na iyaka da China inda kawo yanzu cutar ta harbi mutum dubu 20 da 400 kuma ta hallaka 425, akasari a biranen Wuhan da Hubei inda mahukuntan kasar suka dauki matakin takaita zirga-zirgar jama’a da nufin hana yaduwarta.