Search
Subscribe
Cutar Lassa ta kashe mutum 18 a Kano, Ondo

Cutar Lassa ta kashe mutum 18 a Kano, Ondo

Rahotanni daga Jihar Kano da Ondo na nuna cewa akalla mutum 16 ne suka mutu sakamakon sake bullar cutar Lassa.

A Jihar Kano, cutar ta yi ajalin ma’aikatan Asibitin Aminu Kano guda biyu sakamakon tiyata da suka yi wata mata da aka kawo daga wani asibiti mai zaman kan shi domin haihuwa.

Wadanda suka mutu a Kano akwai Dokta Ummu Khultum Abba, wadda likita ce mai neman kwarewa, sai Dokta Habibu Musa wanda kwararren likita ne a bangaren rage radadi lokacin tiyata.

An ce mai cikin da aka yi wa tiyatar ’yar asalin Jihar Bauchi ce, kuma ita ake zargi tana xauke da cutar, kuma ita ma ta rasu.

A jihar Ondo kuwa, cutar ta yi ajalin mutum 16 ne.

Yanzu haka an tura zuwa Legas domin bincike tare da tabbatar da lamarin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin