✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da gangan muka rufe matatatun mai —NNPC

Barnar kudi kawai ake yi wurin gudanar da matatun.

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya ce da gangan ya rufe matatun man gwamnati duk da biliyoyin Naira da ake kashewa na gyaransu a duk shekara.

Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce an rufe matatun ne saboda fasa bututan mai da barayi suka yi ya sa bututan ba sa iya tura danyen mai da matatun za su tace.

“Ba ma iya tura mai ta wadannan bututan, sun tsufa, amma babban dalilin shi ne girman barnar da masu fasa bututu suka yi musu ya wuce misali”, inji shi.

Saboda haka, a cewarsa, babu hikima a ci gaba da gudanar da matatun, ana kashe musu makudan kudade ba tare da ana cin moriyarsu ba.

Kyari ya sanar da haka ne a yayin gabatar da daftarin kasafin kamfanin na 2021 a gaban kwamitin Majalisar Wakilai.

Shugaban na NNPC ya ce a halin yanzu, layin bututun mai na Excravos da ake kula wa kamfanin da shi ne kadai ke cikin koshin lafiya.

Ya kuma ce NNPC ba zai iya aiki da bututun mansa 100% ba saboda, “Matatun mai na Kaduna da Warri kadai na bukatar gangar danyen mai 170,000 a kullum domin su yi aiki kashi 70%”.

Ya ce a halin yanzu, NNPC na da gidajen mai fiye da 5,000 da manyan ma’ajiya 13 da ke bukatar a ba su cikakken tsaro daga ayyukan ’yan fashi.

“A yanzu, in banda layin bututun mai na Atlas Cove zuwa Ibadan da kuma na Fatakwal zuwa Aba, babu wanda ake yi wa gyara”, inji Kyari.

“Ba ma iya tura mai ta wadannan bututan saboda sun tsufa, sannan barnar da masu fasa bututu suka yi musu ya wuce misali”, inji shi.

Ya ce masu fasa bututu sun ja wa NNPC asarar Naira biliyar 43 a wata shidan farkon 2020 kuma a duk wata barayi na fasa bututun mai sau 80.

Wannan ce ta sa kamfanin ya gwammace ya rika dakon mai daga manyan ma’aijiyansa zuwa sassan Najeriya.

Ya ce kamfanin zai kashe biliyan N314.9 a kan ayyuka a 2021 sabanin biliyan 444.75 na 2020.

Kyari ya kuma shaida wa kwamitin cewa kamfanin ya rasa kudaden shiga da ma wasu ayyukansa sakamakon bullar annobar COVID-19.

Durkushewar tattalin arziki da dokar kulle sun karya farashin mai tare da raguwar hakarsa, baya ga karkata da duniya ta fara yi suwa ga makamashi na zamani.

Raguwar kudaden shiga sun tilasta wa NNPC rage kudaden da take kashewa zuwa kashi 40%, kasancewar ta kasa sauke wasu nauyin da suka rataya a wuyanta na tara kudade da aikace-aikace.

A cewarsa, duk da cewa Najeriya na kokarin kara yawan kudaden shiganta ta bangaren mai, ita ma kamar sauran kasashe ta rungumi amfani da makamashi na zamani.

Don haka ya roki Majalisar Tarayya ta taimaka ta amince da Kudurin Dokar Man Fetur (PIDB).