✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da karin albashi da rage tsadar kayan masarufi wanne ya kamata NLC ta nema?

A makon jiya ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta gudanar da yajin aiki na kwanaki domin tunatar da gwamnati a kan maganar karin albashi.…

A makon jiya ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta gudanar da yajin aiki na kwanaki domin tunatar da gwamnati a kan maganar karin albashi. Wannan ne ya sa a daidai lokacin da wadansu suke murna, wadansu kuma suna ganin karin albashin zai sa farashin kayan masarufi ya kara tsada. Saboda haka  wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan abin da ya kamata kungiyar ta nema, kuma ga abin da suke fada: 

Kara albashi yana da kyau amma akwai illa – Danlami Adhanu

Daga Amina Abdullahi, Yola

Danlami Adhanu: “Najeriya a yanzu mun shiga tsaka-mai-wuya. In ba haka ba, zancen karin albashin nan ya jima ana yin sa. Karin albashi yana da kyau amma illar ita ce da zarar an kara albashi, kaya a kasuwa dole su tashi domin masu sayar da kaya ba su san muhimmancin karin albashin nan ba. Su dai kawai suna ganin tunda an kara albashi ya kamata su kara kudin kaya. In ba haka ba, ni a ra’ayina, na fi son a kara albashi. Koda yake an ce ba mu cika kulawa da tashi ko raguwar kaya a kasuwa ba. Amma abin da ya kamata a yi shi ne, kamar yadda Shugaba Buhari ya sanya kowa ya koma gona, ya kamata kayanmu su zama da sauki fiye da kayan waje yadda za a samu rata da sauki domin yin hakan zai kwadaitar da jama’a sayen kayan gida fiye da na waje.”

Gaskiya rage farashin kaya zai fi alheri – Muhammadu Sabi’u

Daga Isiyaku Muhammed

Muhammadu Sabi’u: “Gaskiya rage farashin kaya zai fi alheri. Me ya sa na ce haka? A halin yanzu, wadansu ’yan Najeriya na matukar fargabar cewa idan aka kara yawan albashi, to akwai yiwuwar farashin kayan ya karu. Amma kuma idan kayan ne aka rage farashinsu, to yana da matukar wahala a rage yawan albashi. Abin nufi shi ne, idan aka kara yawan albashi, watakila garin neman kiba sai a samo rama, wanda hakan zai kara ta’azzara al’amura a kasa. Bugu da kari, kara yawan albashi zai ci gaba da zaftare darajar Naira ta yadda nan gaba za a kasa shawo kan matsalar cikin sauki. Gara tun yanzu a guji karin albashi, sannan a rungumi sassauta farashin kaya, musamman na masarufi.”

Rage tsadar kayan masarufi ya fi muhimmanci – Hussaini Hammangabdo

Daga Amina Abdullahi, Yola

Hussaini Hammangabdo: “Rage tsadar masarufi ya fi muhimmanci domin idan aka kara albashi, farashin kaya za su tashi a kasuwa sannan kudin ba zai yi albarka ba. Kuma ba kowa yake karbar albashi ba. Mun ga tasirin rage karin albashi a 1984 inda talaka zai je shago ya sayi kaya a farashi mai rahusa. Don haka rage tsadar kayan masarufi ya fi.”

Rage farashin masarufi ya fi dacewa – Rukayya Muhammad

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Rukayya Muhammad: “A nawa ra’ayin, abin da ya fi dacewa Kungiyar NLC ta nema a wajen gwamnati a wannan lokaci shi ne a rage hauhawar farashin kayayyakin masarufi.  Idan aka yi haka, zai shafi kowane dan kasa ne, wato da ma’aiukatan da  wadanda ba ma’aikatan gwamnati ba.  Amma idan kungiyar ta karkata akalarta ga bangaren karin albashi ne kawai, to hakan zai shafi ma’aikata ne kawai sauran ’yan kasa kuma ko oho.  Sannan idan aka rage farashin kayayayyaki, ko ba a kara albashi ba abubuwa za su yi  sauki, don dan abin da suke karba zai iya isarsu a wata.”

Mutane kalilan ne suke karbar albashi – Abubakar Haruna

Daga Isiyaku Muhammed

Abubakar Haruna: “Wadanda suke karbar albashi ba su yawa a Najeriya, don haka kara albashin su kadai zai amfana. Amma idan aka rage tsadar kayan masarufi, har su masu karbar albashin za su ji dadi domin albashinsu zai kara daraja.”

 

Karin albashi ya kamata NLC ta nema – Zainab Abdul’azeez

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Zainab Abdul’azeez, dalibar  jami’a. “A nawa ra’ayin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ya dace ta nemi a kara wa ma’aikata albashi ne maimakon neman a rage kudin kayayyakin masarufi saboda dalilai kamar haka: Na farko ko ta nemi a rage kudin kayan masarufi a wannan lokaci, hakan ba zai yiwu ba, don na tabbata da yawa daga cikin ’yan kasuwa ba za su amince ba, don su ma sun sayo kayayyakinsu da tsada ne, kuma ba za su amince a tilasta musu su fadi ba tare da cin riba ba.  Don haka abu mafi sauki shi ne su samar wa ma’aikata mafita wajen kara musu albashi, hakan zai saukaka musu matsanancin rayuwar da suke fuskanta. Don haka kara albashi ne ya fi muhimmanci a wannan lokaci fiye da yunkurin neman a rage hauhawar farashin kayayyakin masarufi.”