✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatar da ayyukan gwamnati ya haifar wa Amurka asara

Tsarin kula da lafiya na shugaban Amurka Barack Obama, wanda aka Turancin kafafen yada labarai aka yi wa lakabi da “Obamacare,” ya haifar wa Gwamnatin…

Tsarin kula da lafiya na shugaban Amurka Barack Obama, wanda aka Turancin kafafen yada labarai aka yi wa lakabi da “Obamacare,” ya haifar wa Gwamnatin Amurka asara. Ta yadda a kullum akan yi rashin Dala miliyan 300, bayan da takadamar ta sanya ayyukan gwamnati suka tsa cika a kasar.
“Ina rokon ’yan Jam’iyyar Republican su bari gwamnati ta ci gaba da gudanar da harkokinta,” a cewar Shugaba Obama, lokacin da yake yin cikakken bayani game da tsarin da ya bullo da shi na kula da lafiya, wanda aka fara aiwatarwa a ranar Talatar da ta gabata.
Shekaru 17 da suka gabata aka taba dakatar da ayyukajn gwamnati a kasar Amurka, saboda ’yan majalisar wakilai da ke karkashin jam’iyyar Republican, sun ki a amincewa gwamnati ta dauki nauyin shirin kula da lafiya da shugaba Obama ta bullo da shi, wato “Obamacare,” a shekarar kudi ta bana. Duk wani yunkuri da ’yan majalisar dattijai suka yi, majalisar wakilai ta ki amincewa da shi. Jam’iyyar Democrat ke da rinjaye a majalisar dattijai, inda kuma ’yan Republican ke da rinjaye a majalisar wakilai.
Majalisar ta kada kuri’a don neman amincewar ta aiwatar da gyare-gyare a kasafin kudi, ta yadda za a samu damar ci gaba da ayyukan gwamnati har zuwa ranar 15 ga watan Disamba, suka kuma bayar da umurnin kada a aiwatar da dokar sabon tsarin kula da lafiyar masu karamin karfi, sannan a janye biyan haraji kan wadansu kayan aikin jinya. Wannan al’amari ya ci tura, majalisun wakilai da dattijai sun yi karo da juna.
dimbin asarar da gwamnatin Amurka ta yi fama da su, sun hada da soke tafiye-tafiyen da Shugaba Obama ya shirya yi zuwa wasu kasashen duniya,  wadanda suka hada da Indonesiya da Malesiya da Filifins, wato a nahiyar Asiya. Sannan a rufe wasu kafofin sadarwa na intanet a kasar, wadanda suka hada da shafukan Twitter.