✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban jami’ar ABU 48 za su samu tallafin Naira miliyan 4.8

Wasu daga cikin daliban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ABU masu hazaka 48, da aka zaba zasu samu tallafin Naira dubu 100 kowannen su daga…

Wasu daga cikin daliban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ABU masu hazaka 48, da aka zaba zasu samu tallafin Naira dubu 100 kowannen su daga tallafin ilimi da gwamnatin kasar China ta bayar.

Wannan tallafin na cikin shirin da Gwamnatin kasar China ta tsara sanadiyyar dangantakar da suka tsara wajen baiwa ‘yan Najeriya tallafi.

A yayin bayar da tallafin kudin mataimakin Jakadan China a Najeriya Mista Zhao Yong wanda ya wakilci jakadan China a Najeriya, Dakta Zhou Pingjiang ya ce wannan na daya daga cikin shirin bayar da tallafin ga daliban jami’ar ABU masu hazaka da aka zaba.