Search
Subscribe
Dalilan da Hausawa suke guje wa darasin Hausa a makarantu

Dalilan da Hausawa suke guje wa darasin Hausa a makarantu

Harshen Hausa na daya daga cikin manyan harsunan duniya ba wai Najeriya kadai ba musamman  ganin yadda harshen ke kara samun karbuwa.

Daga cikin manyan dalilan da suke nuna hakan akwai karuwar kafafen watsa labarai da ke amfani da Hausa a duniya; bayan BBC da Muryar Amurka da aka saba da su, akwai TRT ta kasar Turkiyya da CRI ta China da  RFI  ta Faransa da sauransu.

Sai dai yanzu harshen yana samun koma-baya musamman a makarantun sakandare inda ake ganin daga nan komai zai fara tafiya.

Wani malamin makaranta, Malam Kabir Bala ya ce. “Farko dai idan muka dubi tarihin shigowar ilimin boko a Arewa, sai da aka kai ruwa rana sannan mutanenmu na wancan lokacin suka fara sanya ’ya’yansu. To kuma sai kwadayin koyon Ingilishi ya rika shiga cikin zukata. Sai ya zamo duk wani darasin da za a koyar da Ingilishi ake koyar da shi. Ita Hausar sai ya zamo ana barin darasinta a karshe. Kuma ba a koyar da darasin Hausa sai lokacin da ake gab da tashi a makaranta, yara sun gaji wadansu ma har barci suke yi a lokacin da ake koyarwar.”

Shi ma wani malamin, Malam Nuhu Bidi cewa ya yi. “Idan aka yi jarrabawa, babban abin da iyaye suke fara tambaya shi ne Ingilishi? Da zarar an ce yaro ya ci Hausa kawai sai ka ji an ce Hausar me? To wannan na kara sa yaran su kyamaci darasin. Kuma maimakon idan za a yi magana musamman a tsakanin masu ilimin boko a yi amfani da Hausa saboda yaro ya yi sha’awa, sai a rika yi ana surka kalmomin Ingilishi.” Malam Nuhu ya kara da cewa hatta wadanda ake gani sun yi zurfi a karatun Hausa can farko ba ita ce suka yi niyyar karantawa ba.

Wani dalibi mai suna Yusuf daga Jihar Katsina ya ce, “Gaskiya ko mutum ya karanta Hausa babu inda zai samu wani aiki. Ko tsaron shago mutum zai yi idan aka ce Hausa ya karanta, to gaskiya da wuya ya samu. Amma kana cewa Ingilishi ko lissafi to za a kalle ka koda kuwa wajen aikin da Hausa ake amfani. Da da harshen Hausa ake koya mana darussa a makaranta, shi kuma Ingilishi a rika koya mana kamar yadda ake yi wa Hausar yanzu da mun fi cin jarrabawa.”

Wata daliba mai suna Amina Bashir daga Makaranatar Sakandaren Sani Mainagge a Jihar Kano ta ce yawancin abin da ake koyarwa a darasin abubuwa ne da mutum ya riga ya sani. “Harshen nan fa da shi muke magana tunda aka haife mu, to me muke nema mu iya? Tunda dama ana koyar da shi ne don mutum ya iya magana.”

Sai dai ba kamar sauran daliban ba, shi dalibi Al’amin Muhammad Haruna wanda yake aji biyu na Karamar Sakandaren Magwan da ke Jihar Kano ya shaida wa Aminiya cewa shi yana son darasin Hausa saboda yana fahimtar abin da ake koyarwa sosai. “Hakan ya janyo ban taba faduwa a jarrabawar darasin ba,” inji shi.

Malama Binta Yusuf da ke koyar da darasin Hausa ta shaida wa Aminiya cewa a gaskiya yawancin dalibai ba su son darasin Hausa, don suna ganin gazawa ce su koyi Hausa, “Saboda suna ganin harshensu ne, don haka ba su tsayawa su koya. Abin takaici a cikin lamarin shi ne sai sun rubuta jarrabawar sai ki ga mutum bai ci ba. Da yawa daga ciki sai ki ji suna cewa wai dama su ba su iya Hausar ba, bayan shi ma Igilishin ba iyawa suka yi ba,” inji ta.

Malama Binta ta dora alhakin wannan lamari kan makarantu masu zaman kansu inda ba su ba darasin Hausa muhimmanci domin akwai ajujuwan da ba a koyar da darasin gaba daya.

Shi kuwa Malam Salisu Abdullahi dora alhakin kin darasin Huasa da dalibai ke yi ya yi a kan iyayensu. “Yawanci iyaye ne ke karya wa ’ya’yansu gwiwa, sai yaro ya zo gida yana murna ya ci darasin Hausa sai iyaye su gwale shi. Don haka sai yaro ya fara tunanin ashe ma darasin ba ya da muhimmanci don haka sai ya fara yi masa daukar sakainar kashi.”

Da yake jawabi,  malami a Tsangayar Fasahar Harsuna da Al’adun Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Malam Adamu Ibrahim Malumfashi ya bayyana cewa babban dalilin ya yake sanya dalibai suke guje wa darasin Hausa tun daga matakin sakandare har  zuwa jami’a shi ne jahiltar muhimmancin karanta harshen da iyayensu suka yi tun farko.

Malam Adamu Malumfashi wanda tsohon Editan Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ne ya ci gaba da cewa, “Har yanzu wadansu iyaye kwakwalwarsu tana tsammani muna karkashin mulkin mallaka ne, saboda haka wannan kyama da iyaye suke nunawa kan ’ya’yansu su karanta Hausa ta kai wadansu iyayen ma ba sa barin yaransu su karanta ko ilimin addinin Musulunci. Wai su a zatonsu ci gaba ko daukaka sai ka karanta wani fanni na kimiyya ko kuma Ingilishi.

“Amma ni a matsayina na malami sai in dauki irin wadannan iyaye jahilai, domin idan da sun san cewa a halin yanzu a duniya babu wata kasa da ta ci gaba alhalin tana amfani da harshen aro. Misali in ka dauki Amurka da Ingilishinta, Jamus da Jamusancinta, Faransa da Faransancinta, Ingila da Ingilishinta, China da Sinancinta kai hatta na baya-bayan nan da suka ci gaba irin su kasar Iran ita ma da Iraniyancinta haka kuma Turkiya da Turkancinta take amfani,” inji shi.

Malam Adamu Malumfashi ya ce wannan kyama ce take naso ta biyo dalibai har zuwa matakin jami’a inda za ka ga samari suna jin kunya a ce harshen Hausa suke karantawa. “Lokaci ya yi da iyaye za su gane cewa harshen Hausa ya kai bantensa a duk fadin duniya don ya isa mai hankali misali yadda manyan kasashen duniya suke da gidajen rediyoyi na Hausa wadanda kuma akasari idan ka duba za ka ga wadanda suka karanta harshen Ingilishi ne da wasu kwasa-kwasan ke yin kaka-gida suna cin gajiyarsu ba  daliban Hausar ba,” inji shi.

Wata daliba mai nazarin Harshen Ingilishi a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya mai suna Fatima Muhammad da take amsa tambayar Aminiya kan da lokacin da ta nemi shiga jami’a don nazari Harshe Ingilishi an ba ta Harshen Hausa ko za ta yi hakuri ta ci gaba da karanta shi? Sai ta ce “A gaskiya ba zan karanta shi ba, saboda ina ganin kawai bai dace a ce na karanta Hausa ba. Domin duk wanda yake karanta Hausa ana ganinsa kamar ba wani abu yake karantawa ba, don ba a dauke ta da muhimmanci ba.”

Shi wani malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Malam Audu Auwalu Sarkin Fulani ya ce yana gani dalilai uku ne manya suke sanya haka. “Na farko akwai makomar wanda ya karanci harshen Hausa da iyaye da kuma su daliban suke dubawa. Ka san cewa a halin yanzu duk wanda ya yi karatu a nan kasar yana sa ran zai yi aiki ne a wata ma’aikata mai maski. Haka ya sanya masu irin wannan ra’ayi suke ganin ai idan sun karanta Hausa ba su da wata makoma a irin wadannan wurare. Na biyu shi ne tafiya da zamani, idan ka lura duniya ta canja kusan komai a na’urar kwamfuta ake nazarinsa. Za ka dalibai masu nazarin wasu fannoni sun fi son suna kwance a kan gadajensu su yi bincike a kan karatunsu ta wayar hannu ko kwamfuta, ba sa son zuwa dakunan karatu. To ka ga kuwa har yanzu an bar mu a baya, babu isassun bayanai da dalibi zai iya samu a Intanet wadanda suka shafi nazarin Harshen Hausa,” inji shi.

Ya ce “Sannan dalili na uku shi ne rashin jajircewa daga mu malaman Hausar, za ka shi kansa malamin Hausa labewa yake yi a duk wasu harkoki na yau da kullum ko da jami’ar ce. Da dama suna jin tsoron yin Ingilishi ko da a gaban dalibansu ballantana kuma a ce a wajen taro. Wannan babban kuskure ne a ce ga malami mai nazari tare da koyar da harshe amma wai in ban da harshensa babu wani harshe da zai iya magana da shi. Kamata ya yi akalla a samu malamin harshe yana iya magana da harsuna akalla uku ko hudu. Don haka shi ya sanya ni ba na goyon bayan koyar da Hausa da Hausa da ake yi yanzu a jami’o’i.”

Wani dalibi mai suna Muhammad Ali Ja’e ya ce tun daga matakin firamare dalibai suke raina koyon Harshen Hausa ganin cewa ai harshensu ne na gida wanda kowa da kowa ya iya.

Zainab Ahmad Suleiman wata daliba da take a shekarar karshe a Jami’ar Ahmadu Bello ta ce  tun a matakin sakandare ana mayar da darasin Hausa kamar cinsa banza barinsa banza, don haka babu mai mayar da hankali ga koyonsa.

A nata bayanin, wata malama a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya Dokta Hauwa Muhammad Bugaje ta  ce, “Ni a matsayina na malamar jami’a mai koyar da Harshen Hausa ina ganin akwai dalilai da dama da suka sanya ake samun koma baya wajen nazarin harshen.

“Na daya akwai matsalar ita kanta Hukumar Ilimi ta Kasa. Tunda yake a kundin tsarin mulkin kasar nan akwai dokar da ta ce a karantar da yara da harshen iyayensu tun daga makarantar firamre zuwa karamar sakandare. Amma sai ga shi yau hukumar tana kallo kusan ana neman ma a hana koyar da darussan harsunan gida a makarantunmu. Na biyu kuma akwai matsalar iyaye masu ganin yaya za a ce yaro ya tashi da Hausa a gida Hausa a makaranta. Su a nasu tunani ko a magana a gida sun fi son su yi wa ’ya’yansu magana da Ingilishi. Don haka sai su nuna wa ’ya’yansu cewa Hausar nazarinta ba komai ba ne,” inji ta.

Dokta Bugaje ta ci gaba da cewa, “Mu kanmu da muka karanci Hausar ba ma yi wa Hausar gata da hidima, kamar yadda Malam Akilu Aliyu ya bayyana a cikin wakarsa ta Hausa Mai Ban Haushi. Wanda hakan ya sanya ko gajiyar Hausar ma wadansu ne can a gefe wadanda ko Hausar ba ta ishe su ba suke ke ci. Dubi maganar ayyukan fassara da na tallace-tallace a kafofin watsa labarai.

“Sannan su kansu daliban da suke nazarin Harshen Hausa ba tutiya da karsashin nazarin Harshen Hausar suke yi ba. Domin da yawansu sun nemi wasu kwasa-kwasan ne  da ba a ba su ba aka tura su nazarin Hausa. Wadansu kuma daliban masu nazarin Hausa dama sun shigo jami’a ce kawai don suna son su samu takadar shaidar kammala jami’a,” inji ta.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin