✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da mutanen Kano suka kaurace wa motocin ‘Kanawa Bus’

Duk da cewar motocin kyauta za ake hawan su, wasu sun gwammace biyan kudinsu don biyan bukata a kan lokaci.

Tun ranar Litinin motocin Kanawa Bus Service da Gwamnatin Kano ta bayar domin daukar mutane kyauta suke yawo a kwaryar birnin Kano, amma tsirarun mutane ke shigar su.

A karshen makon da ya wuce ne Gwamnatin Kano ta bayyana cewar manyan motocinta na ‘Kanawa Bus Service’ za su rika jigilar mutane a jihar kyauta.

Gwamnatin Jihar ta ce ta yi hakan ne domin rage wa Kanawa radadin rashin kudi da ake fama da shi kan batun sauyin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

Sai dai kuma wasu jama’ar na zargin akwai lauje cikin nadi, ganin cewa tagomashin na gwamnati na zuwa ne a lokacin da ake tsaka da yakin neman zabe.

Wasu na zargin motocin gwamnatin da bata lokacin fasinjoji.

Aminiya ta zaga don gane wa idanunta wainar da ake toyawa kan yadda Kanawa ke hawa motocin, inda ta ga suna kaurace wa motocin.

Da fari dai Aminiya ta zanta da wani direban babbar motar mai suna Babangida Sule a madakatar motar da ke Kabuga, sai dai ya ce ba kasafai mutane ke hawa motar ba saboda gudun bata lokaci.

Yadda direban motar ke kiran mutane su hau motar kyau

“Da yawan mutane ba sa son hawa saboda gudun bata lokaci.

“A ranar Litinin da muka fito don daukar mutane watakila ba su san kyauta ake hawa ba shi ya sa a ranar ba a samu mutane ba.

“Amma yau idan ka duba cikin motar za ka ga akwai mutane sai dai ba su da yawa.

“Hakan idan muka dan samu mutane sai mu tafi a hanya ma idan mun samu sai mu kara.

“Yanzu daga nan Kabuga har Bata za mu je daga nan kuma mu wuce tashar ’Yan Kaba” in ji direban.

Amma ya ce da safe da yamma motocin sukan cika sakamakon yawaitar masu hawa.

“Da safe mutane da yawa suna hawa, amma gaskiya yara ’yan makaranta ne suka fi hawa.

“Da yamma kam ana cika ta makil, saboda wannan lokacin ’yan kasuwa sun tashi, kuma ana samun karancin abun hawa, don haka wasu su kan hau saboda rage hanya.”

Motar a tsaye ana jiran mutane su hau

Aminiya ta ji ta bakin wasu ’yan mata guda biyu, wadanda dalibai ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Kano, kan dalilin da ya sa suka hau motar.

Laila Sulaiman Umar, daliba ce kuma ta shaida wa Aminiya cewa, “Mun gama lacca ne kuma gida zan tafi yanzu ina fitowa sai na ji direban yana cewa kyauta ce, wannan dalilin da ya sa na hau ko ba komai kudina za su huta.”

Ita kuwa Sadiya Ado cewa ta yi “A Mandawari zan sauka, kuma ta hanyar unguwarmu za a bi tun da ba ni da nisa shi ya sa na hau.

“Da safe na ga yara suna ta hawa amma ban san cewar kyauta ba ce,” a cewarta.

Shi kuwa wani magidanci, Tahir Saleh, cewa ya yi ya hau motar ne saboda an ce kyauta ce, amma ya ce ya san hakan na da nasaba da siyasar da ke tafe.

“Na san dai ba zai wuce ganin zabe ne ya sa aka fara daukar mutane kyauta ba, saboda tun a baya ba a yi hakan ba, kuma mutane sun ki karbar motocin, amma duk da haka zan hau saboda kudinmu ne.

“Da sauri nake yi don komawa gida ba zan hau ba, akwai tsaye-tsaye da yawa saboda jiya na hau daga Bata zuwa bakin asibiti amma an tsaya ya fi sau 30, don haka akwai bata lokaci a irin wannan motar.”

Ita kuwa wata dalibar Jami’ar Bayero ta Kano, mai suna Sailuba Idris da ba ta samu hawa motar ba ta bayyana mana ra’ayinta game da motar.

“Wallahi yau da wuri na fito daga makaranta saboda na samu hawa motar nan, amma ina zuwa aka ce ba ta jima da tafiya ba. Amma zan dan jira ko wata za ta zo tun da nan ce madakatarsu.

“Gaskiya dai unguwarmu da nisa a can Hotoro nake, ka ga idan na hau motar nan kyauta na samu ragi sosai saboda gobe zan samu rarar kudin makaranta.

“Da Allah zai taimake mu su mayar da motocin na daukar dalibai da mun huta sosai wallahi, saboda wani lokacin da safe ana wahalar abun hawa.”

Idan ba a manta ba wadannan dogayen motocin na gwamnatin jihar, karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce, ta samar da su ne da zummar rage yawaitar kwararar babura masu kafa uku, wadanda aka fi sani da ‘Adaidaita Sahu’ a wasu titunan jihar.

A watan Nuwamban 2022 ne, Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta fitar da dokar haramta wa baburan adaidaita sahu bin wasu manyan tituna.

Sai dai dokar ta janyo rudani, lamarin da ya haifar da tsaiko ga harkokin yau da kullum a jihar.

KAROTA ta sahale wa manyan motocin ‘Kanawa Bus Service’ kadai ne bin titunan da aka haramta wa masu baburan na Adaidaita Sahu.

Amma kwana daya kacal da ayyana dokar gwamnatin jihar ta yi mi’ara koma baya, ta janye ta.