Da Dumi Dumi

Dalilin da na farde marainan saurayina – Budurwa

Wata budurwa da ake zargi da farde marainan saurayinta tare da sossoka  masa wuka a Jihar Kaduna a lokacin da ta yi yukurin kashe shi do ta huce haushi kan yaudararta da ya yi ta shiga hannun ’yan sanda.

Budurwar mai sana A’isha Abdullahi mai shekara 22 da take zaune a gida mai lamba A41, Layin Jos a Tudun Wadan Soba, ta yi yukurin kashe saurayin nata ne mai sana Musa Abdullahi, wanda yake zaune a Layin Zariya a Karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.

A’isha Abdullahi ta ce ta yi yunkurin kashe saurayin nata ne saboda daukar fansa da huce haushin yaudararta da ya dade yana yi.

“Kuma na yi haka ne ba tare da shawarar kowa ko sa hannun kowa ba, kamar yadda na ji ana cewa wai ni da wadansu ne muka aikata haka. A’a, ni ce na yi yunkurin kashe shi, domin daukar fansar tsawon lokacin da ya yi yana cutar da rayuwata, yana ta lalata da ni kuma ya hana ni yin aure,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa “Ya dade yana lalata da ni kuma har sau biyu yana zubar mini da ciki. Bayan ya gama bata rayuwata sai kuma ya komo yana bata ni a gari, cewa wai ya ki aurena ne saboda ba ni da tarbiyya.

ADVERTISEMENT

Na yi shirin daukar fansa, na shirya yadda zan yi. Sai na tanadi zobo, na hada da maganin bera domin in ba shi ya sha. To a ranar Talata da misalin karfe 8:30 na dare sai ya kira ni, cewa mu tafi inda muka saba zuwa yana lalata da ni. Bayan mun isa sai na ba shi zobon da na sa magani sai ya ce ya ji zobon yana wani wari-wari, don haka idan ya sha zai yi amai; sai ya ki sha. To, da na ga bai sha ba, sai na amince masa na ba shi kaina kamar yadda ya saba. Sai ya dauko allurar hana haihuwa ya yi mini kuma na saki jiki da shi domin in same shi a daidai,” inji ta.

Ta ce: “Kuma tun daga abin da zai kai mu, ai ka san ba za mu je da kowa ba; don haka daga ni sai shi. Don haka ni ne na yi masa haka ba tare da sa hannun kowa ba kuma ba inda zan gudu, ina nan!”

Yayan A’isha mai suna Aliyu Abdullahi Adamu, wanda aka fi sani da Aliyu Karami ya ce, “Aisha kanwata ce, uwarmu daya ubanmu daya. To, akwai wani yaro mai sana Musa Abdullahi, wanda ya dade yana soyayya da ita tsawon lokaci. Don haka da aka nemi ya fito sai ya ki fitowa, sai aka gane cewa ba ya da niyyar aurenta. Kan haka sai aka nemi ya rabu da ita. Mun zauna tare da danginsa da namu, aka yi alkawari a rubuce cewa Musa ya cire hannunsa a kan A’isha. A lokacin har shi Musa yana kuka da hawaye, ya yarda da alkawarin da aka yi.

“To, daga nan sai aka ce za a hada ta da wani dan uwanta, wato a daura mata aure da shi kuma akwai ’yan uwanta mata uku da za a aurar a lokacin. Sai ta tsere, muka kwashe kusan wata uku babu wanda ya san inda take kuma duk mun san cewa da sa hannun Musa, amma sai muka hakura, ba mu dauki wani mataki na hukuma ba,” inji shi.

Ya ce, “Bayan ta dawo gida sai mahaifinta ya dauki zafi matuka amma sai muka lallashe shi ya hakura. To, idan na yi tafiya tana kwana a gidana ne tare da iyalina, to sai na kara ganinta da Musa. Na kira ta na ce, A’isha ashe har yanzu kuna tare da Musa, har kin manta da irin halin da kika samu kanki a ciki na wulakanci da wahalar rayuwa tare da fushin iyayenki da muka shiga? Sai ta ce wai zai aure ta ne, domin wai ya gane ya yi kuskure, don haka a manta da abin da ya faru a baya.”

Yayan ya ci gaba da ce, “Ni kuma jin haka sai na nemi yayyensa biyu Alhaji Kasimu Abdullahi da Alhaji Hamza Abdullahi na sanar da su. Suka yi godiya tare da alkawarin cewa duk abin da aka yi za su neme ni.

To bayan sun zauna sai suka ce za su zo a sa musu rana, muka aje cewar ranar Asabar. Muka jira su shiru, ba su zo ba. Da na kara tuntubarsu sai suka ce bari su gaya mini gaskiya, Musa dai ya ki ba su hadin kai. Don haka wannan magana sun cire hannunsu.”

Ya ce da suka ji wannan magana daga ’yan uwan Musa ne ya sa ita A’isha ta dauki doka a hannunta. “Kuma hakan ba daidai ne ba, domin ai da ta bi hanyar da ta dace na sanar da hukuma da ya fi. Kuma sai yanzu muke jin cewa a can baya ya zubar mata da ciki har sau biyu, lokacin da ta gudu, kuma wai har wata allurar hana daukar ciki yake mata; da yake shi ma’aikacin kiwon lafiya ne,” inji shi.

Aminiya ta ziyarci Musa Abdullahi a Asibitin Mana’i da ke Unguwar Nagoyi a Zariya, inda yake kwance yana jinyar ’ya’yan marainansa da aka farke. Sai dai ya musanta wasu daga cikin bayanan da A’isha da dan uwanta suka fada.

Ya ce, “A gaskiya ni ban taba daukarta na boye ba kuma bayan an shiga tsakanina da ita, duk na share lambar wayarta kuma na daina nemanta. Ita ce ma take ta bibiyata tana shiga cikin ’yan uwanta domin in aure ta amma ni na fita harkarta.”

Ya ce a ranar da wannan abu ya faru, ya fito ne za shi sayen wani abu a shago, sai ta gan shi. Ta kama masa riga, cewa wai babanta na kiransa. “Don haka sai na bi ta zuwa gidansu amma sai na ga ba hanyar muka bi ba. Tun daga nan hankalina bai ba ni ba. Ta kawo lemo ta ce in sha, sai na ji yana wari sai na ki sha. Na ce a zuciyata in tashi, idan na sha zan yi amai. Muna cikin haka sai ga wadansu mutum biyu sun rufe fuskarsu. Don haka ban san ko su wane ne ba. Suka kama ni, suka rufe ni da karfi cewa sai na sha lemon nan. Da na ki sha sai ta fito da wuka ta farke ni a maraina, ta kuma soka min a goshina. Da na yi yunkurin tarewa sai ta sare ni a hannuna. Daga nan sai suka gudu suka bar ni har na fito wurin da jama’a suke. Aka dauko ni zuwa asibiti, amma duk abin da aka fada ba laifina ba ne.”

Wani ma’aikacin asibiti ya ce likitan da ya kula da shi lokacin da aka kawo shi ba ya nan. Ya shaida wa Aminiya cewa, “Amma dai kusan duk raunin da ya samu da sauki har da ’ya’yan marainansa su ma da sauki, domin ba su yi lahani sosai ba. Ta dan dai goge shi ne kadan kawai, don haka da sauki.”

Wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a binciken da aka fara sun gano, shi kansa mai karar mai laifi ne, domin ya cutar da yarinyar kuma ita ba ta musunta abin da ta yi ba. Ya ce kuma duk wani abin da ta yi, ta fada har da maganin beran da ta sa a zobo ta fada, da kuma wukar da ta yi amfani da ita; duk ta bayar har da allurar hana haihuwa da yake yi mata duk mun dauka. “Kuma har likitan da yake zubar mata da ciki, shi ma ya zo hannu. Kuma a bayyanan mutanen gari, kusan duk sun ba ta goyon baya saboda sanin halin shi Musa. Ka san kauye, duk wani abu da ya faru, za ka samu bayaninsa a fili,” inji shi.

Shugaban Shiyya na ’Yan sandan da ke Soba, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce wanda aka yi wa raunin yana asibitin, ita kuma yarinyar tana hannunsu suna bincike kafin daukar mataki na gaba.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya