✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da PDP ta fadi zabe – Godknows Igali

Wani jigon a Jam’iyyar PDP a Jihar Bayelsa, Mista Godknows Igali, ya bayyana dalilan da ya sa jam’iyyarsu ta rasa kujerar Gwamnan Jihar, inda ya…

Wani jigon a Jam’iyyar PDP a Jihar Bayelsa, Mista Godknows Igali, ya bayyana dalilan da ya sa jam’iyyarsu ta rasa kujerar Gwamnan Jihar, inda ya ce alamu sun nuna yiwuwar haka tun farko,

Igali wanda ya zanta da manema labarai ya ce abin da ya sa APC ta karbe mulkin Jihar Bayelsa shi ne yin watsi da mulkin karba-karba da ake yi a jihar, wanda ta sa na rika jan kunnen ’ya’yan jam’iyyar.

Tsohon Babban Sakataren a tarayya ya ce Jam’iyyar PDP ta mike kafafuwanta tana ganin cewa babu abin da zai sa ta fadi a zabe, amma a karshe ta sha kaye a jihar da ba ta taba rasawa ba.

Igali ya ce kowane bangaren Jihar Bayelsa ya samu mulki daga lokacin Cif Diepreye Alamieyeseigha da Goodluck Jonathan da Timipre Sylba zuwa Seriake Dickson wanda ya fara yin shekara takwas a Gwamna.

Igali ya nuna yadda na kusa da Gwamna Dickson suka nemi su yi watsi da tsarin karba-karba, inda irin su Sylbester Ikoli da Dabid Alagwa da Fred Agbedi suka yanki fom din takara a PDP.

Don haka ne aka bada dama wannan karo mulki ya koma ga mutanen tsakiyar Bayelsa. Igali ya kara da cewa an fito da mutumin Kolokuma a zaben Sanata da tunanin za a ba mutanen Ijaw Gwamna. Sai dai kuma ba haka aka yi ba, duk da cewa Sanatan Tsakiya ya fito daga karamin garin Kolokuma, sai aka hana ’yan siyasar Ijaw takarar Gwamna a karkashin PDP.

Wakilinmu ya ce Jihar Bayelsa ta kasance jiha ta biyu a Kudu maso Kudu a shiyyar da Jam’iyyar APC ta karbi ragamar jihar a zabe.