Daily Trust Aminiya - Dalilin da ya sa nake son barin kulob din Liberpool -Luiz Su
Subscribe

Dalilin da ya sa nake son barin kulob din Liberpool -Luiz Suarez

 Luis Suarez cikin tunani yadda zai bar kulob din LiverpoolShahararren dan kwallon kulob din Liberpool da ke Ingila Luiz Suarez a shekaranjiya Laraba ya bayyana dalilin da ya sa yake neman barin kulob din.
Suarez, wanda kulob din Arsenal ya dage wajen yin zawarcinsa kafin a fara kakar wasa ta bana, ya ce babban dalilin da ya sa yake neman barin kulob din a wannan lokaci shi ne, yarjejeniya ce suka yi a tsakaninsa da kulob din a kakar wasan da ta wuce cewa muddin kulob din ya kasa hayewa gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (UEFA Champions League) zai amince masa ya canza sheka.
Ya ce wannan yarjejeniya a rubuce suka yi ta a tsakaninsa da kulob din, don haka abin ya daure masa kai a wannan lokaci da kulob din yake neman yi masa kafar ungulu a yunkurin da yake na neman hana shi tafiya kulob din Arsenal da ke Ingila.
Suarez ya kara da cewa, “ba ni da burin in ci mutuncin kulob din Liberpool da magoya bayansa musamman ganin yadda muka yi zaman mutunci”.
Suarez ya ce a bara ya yi alkwarin taimaka wa kulob din hayewa gasar zakarun kulob-kulob na Turai amma tun da hakan ba ta samu ba yakamata mu mutunta yarjejeniyar da ke tsakaninmu, yin haka shi ne dattako. “Amma muddin suka yi biris da bukatata ko shakka babu zan kai su gaban kuliya”.
A halin yanzu dai kulob din Arsenal ya nace sai ya sayi Luiz Suarez ko ta halin kaka.  Hasalima a makon da muke ciki ne ake sa ran dan kwallon zai shigar da karar kulob din Liberpool a kokarin da suke yi na neman hana shi tafiya.
Tuni dan kwallon ya aika da bukatar neman barin kulob din Liberpool da hakan ta sa a dokar Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, tilas kulob din ya kyale shi ya canza sheka.

texem
More Stories