✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin hadewarmu  don kawar da Gwamnan Bauchi – Bello Kirfi

A makon jiya ne Alhaji Muhammadu Bello Kirfi Wazirin Bauchi ya hado kan wadansu manyan ’yan siyasa da suka hada da Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu…

A makon jiya ne Alhaji Muhammadu Bello Kirfi Wazirin Bauchi ya hado kan wadansu manyan ’yan siyasa da suka hada da Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da manyan ’ya’yan Jam’iyyar APC da suka hada da Dokta Ibrahim Yakubu Lame da Kyaftin Bala Jibir da ’yan takarar Gwamnan Jihar na PDP da PRP da PDM da GPN inda suka kulla kawance don kawar da Gwamnan Jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar. Mene ne ya yi zafi, ya bayyana dalilin haka. Sai dai Alhaji Aliyu Yerima Giyade daya daga cikin dattawan Jihar Bauchi daya rike Mukamai dabam dabam na kwashina a jihar, yana kuma daya daga cikin dattawan jihar kuma wakili a Majaliasar Bayar da Sharwari ga Gwamnan Bauchi ya jagoranci wadansu ’yan siyasa da suka hada da Alhaji Sanusi Baban Takko (Barayan Bauchi) inda suka mayar da martani suna masu cewa hadakar ta son zuciya ce kawai:

 

Me ya sa kuka yi wannan gangami?

Mun hadu ne don mu yaki Gwamnan Jihar Bauchi wanda ya nace sai ya koma kan karagar mulki a karo na biyu. Kuma cikin maganganun masoyanmu da suke tare da mu, mun gaya muku muna tare da Allah, domin ba za mu ce mun fi kowa son Bauchi ba, amma in kun dubi halin da Bauchi ke ciki a yau in muka zauna ina tabbatar muku Allah zai yi fushi da mu. Ni ba na neman wani abu, ba na neman wani mukami na yi Minista sau biyu, na yi Babban Sakatare Allah Ya ba ni ’ya’ya masu albarka, ya kamata a ce in zauna in huta a gida a wannan lokaci amma mutanen Bauchi ba su gaji su fito su yi fuska-da-fuska da mutumin da ba ya da gaskiya ba.

Daga dama Shugaban Majalisar Wakilai Hon. Yakubu Dogara sai Alhaji Bello Kirfi sai xan takarar Gwamna a Jam’iyya PRP Farfesa. Ali Pate da takwaransa na PDP Sanata Bala Mohammed a wurin taron manema labarai da suka kira

Akwai zancen talauci wanda hakan yake sa a bai wa mutum Naira biyar ko goma ya canja ra’ayinsa don abin da zai samu, wannan dan kudi bai isa abincinsa na rana guda ba, kuma saboda rashin zuciya da rahin sanin ’yancinsu na rayuwa sai ka ga an yi yadda ake so da su. Wasunku sun ga irin yadda aka yi manakisa a zaben fitar da gwani a bara (a Jam’iyyar APC), ba mu ji dadinsa ba inda karfi da ya ji aka danne abubuwa wannan shi ne babban abin da ya sa muka kafa wannan kawance, cikinmu akwai sauran mutane daga jam’iyyu daban-daban da wannan jam’iyya tamu.

Saboda an lura da yadda yawancin mutane a cikin APC suka ci zaben fitar da gwani aka zo aka canja aka hana su damar kamar a mazabata wanda ya zo na karshe a zaben fid da gwani na dan Majalisar Wakilai shi aka ba.

Saboda ire-iren wadannan rashin gaskiya da murdiya da kin yi wa al’umma aiki ya sa muka ce mu hadu mu yi kokari don ceto jiharmu saboda mun tabbata muna tare da Allah, ina ganin Allah Ya tsara rayuwata watakila zanyi irin wadannan ayyuka ne muna rokon Allah Ya ba mu sa’a.

Wadanne matsaloli ne suka kuke kin Gwamnan ya koma karo na biyu?

Daga cikin matsalolin akwai na rashin ilimi, tun kafin Boko Haram mu ne a baya a fagen ilimi, yanzu kana fita Kofar Gombe akwai Babbar Sakandare in ka shiga za ka ga yara a kasa suke zaune babu kujerun zama balle kayan aiki, akwai kudin da ake bayarwa da abin da shi Gwamna ya kyautu ya bayar game da ’yan makaranta amma yadda ake abubuwa ba yadda mutane suke so ba ne. Akwai batun kudaden shiga, Bauchi ba mu da wata masana’anta, kamfanin da muke da shi na harhada motocin noma na Steyr wanda ya dade da suma, an zo aka sayar ina daya daga cikin wadanda suka tara gudunmawar kudi domin wadansu mutanen wajen jihar ce za su saya, saboda kishi muka ce gwamma mu harhada kudi, mu sayi kamfanin amma abin bakin ciki babu goyon baya daga Gwamnan da daukacin gwamnoninmu na Arewa wadanda suke da jari a kamfanin. Gwamnanmu mun je wajensa da takarda da komai, ya yi mana alkawarin cewa ba zai je waje ya sayo wasu abubuwa ba sai in mun kasa bayarwa, to ba mu samu kishi daga gwamnonin Arewa ba musamman na Bauchi.

Yau tafiye-tafiyen da ya yi babu iyaka ya ce mana ya sayo motocin huda 500 lokacin da Shugaban Kasa Muhammafu Buhari ya zo an gwada biyar ba mu san ya sayo ba, bayan biyar din da aka gwada har yau ba sauran ku tambaya sun iso? Jama’a za su ce muku a’a ba su iso ba!

Duk hedkwatocin jihohin Najeriya Bauchi ta fi ko’ina kazanta kafin ka fita daga Bauchi daga titin Wunti za ka ga tarin shara ko’ina in ka fita gefe-gefe kuwa za ka ga shara kamar dutse, akwai masu kwashe shara  da watakila ana ganin su jifa-jifa.

Daga cikin wadanda suka mulki Jihar Bauchi a farar hula Tatari Ali shi ne gwamnanmu na farko, ya yi iyaka kokarinsa lokacin ma babu kudi, shi ya kawo mana kwalta cikin garin Bauchi shi ya sa mana lantarki a garin Bauchi, ya yi hanyoyi har zuwa kasar Hakimin Duguri, ya kuma yi hanyoyi da wutar lantarki a kasar Katagum da yankin Misau da Gombe lokacin tana Jihar Bauchi.

Lokacin da aka zo zabensa na biyu ina daga cikin shugabannin jam’iyya sai muka hadu muka ce to mutumin nan ya yi kokarinsa saboda haka babu zancen a yi zaben fid-da-gwani mu bar shi ya kara shekara hudu, haka muka bar shi aka sake zabensa  saboda haka ina gaya muku wannan labari ne don ku sani mu ba muna kin M.A. Abubakar ba ne. Ya zo mun karbe shi hannu bibbiyu inda ya zo domin yi mana aikine da ba laifi, amma ya zo ya ki yi mana aiki babu aiki ko da daya da ya fara ya kare, mu wanda duk zai yi mana aiki shi ne namu.

Gaskiya abin da muka fadi cikin takardar da muka karanta ba karya ba ne, mu dattijai ne ba mu so mu yi karya amma abin da Jihar Bauchi ta samu ya haura Naira biliyan 50 (a zamaninsa) saboda ba mu so mu yi karya amma ya yi kusan Naira miliyan 100, akwai kudin Kulob din Paris, akwai na taimako daga Gwamnatin Tarayya akwai kason da ake bayarwa kowane wata watakila shi ma in aka tara shi kawai ya haura Naira miliyan 50. Mun dai yi ne don nuna misali kuma kun sani ba wani aiki da aka yi a Jihar Bauchi, dubi hanyar nan ta wajen Babban Banki zuwa Unguwar Gidajen Gwamnatin Tarayya (Federal Low Cost) daga hawansa kan mulki bai kai wata shida ba aka soma aikin nan har yanzu ba a kare ba. Kuma na samu labari don ban cika zama da yawa a nan Bauchi ba, nakan je wurare inda zan samu tsoffafi irina irin su Kaduna mu rika dan yin hirarmu.

Ana ganin kuna wannan abu ne don wadansu na zargin cewa Gwamnan ba mutumin Bauchi ba ne?

Wadansu suna cewa ba mutumin Bauchi ba ne wannan duk maganar banza ce. Aka turo mana sojoji wadanda ba wani abu tsakaninmu suka zo suka yi aikinsu suka tafi. Mu Bauchi ba mu da kyamar baki in ma bakin ne, akwai wadanda muka sani ni na kammala karatu a 1950, na gama makarantar da ake kira Middle School kuma na yi ritaya daga aiki a karshen 1979, saboda haka akwai wadansu wadanda aiki ya kawo su Bauchi, suka zauna har sun kai mukamin Babban Sakatare a aiki bai dame mu ba. Saboda haka wanda ya zo ya dan yi mana aiki daidai gwargwado za mu gode. Ahmadu Mu’azu ya zo ya yi iyaka kokarinsa, Isa Yuguda ya zo bai yi aiki isasshe yadda ya kamata ba kuma laifinsa yana da wani hali wanda yake in ya riga ya sa zuciyarsa a kan abu dole sai ya yi. Yadda Isa ya zo ya samu Bauchi ya taimaka ya samu kudi an yi amfani da kudi ya dan rarraba haka, amma kuma watakila lokaci zai zo ko da yake bai kyautu in fadi a nan ba wanda za a nemi wadannan kudi.

Saboda haka ni kaina a lokacin da yake son komawa karo na biyu na shiga na yi iyaka kokarina muka taimaka masa ya dawo ya yi mulki a karo na biyu, to amma fa yadda ya fita akwai ’yan kudade na bashi wadanda bai wuce mako biyu ko uku ba ya bar gwamnati kudin bashi ya zo ba mu san yadda wadannan kudade suka shiga ba. Saboda haka mu din nan musamman ma ni abin da duk kuka ga nake yi ina rakiya ne ni na riga na gama. Ina godiya ga Ubangiji Allah, tunda ni ba mai kudi ba ne amma ina da rufin asiri, in na gaza Allah Ya ba ni ’ya’ya wadanda za su tallafa mini ni da iyalina, har zuwa iyakar da Allah Ya nufa.