✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin janye wa hukumar yaƙi da rashawa ta Kano jami’an tsaro — ’Yan sanda

An umarci ‘yan sandan da aka gama tantancewa da su gaggauta komawa bakin aiki.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta yi ƙarin haske dangane da dalilin janye jami’anta da ke samar da tsaro a hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar.

Rundunar ta ce an ɗauki matakin ne saboda za a yi aikin tantance yawan ‘yan sandan da ke ƙarƙashin hukumar da kuma fahimtar yanayin ayyukansu tun daga shekarar 2015 da aka tura su aiki a hukumar kawo yanzu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a wannan Juma’ar.

Sanarwar ta ce za a tantance su ne bayan rahotannin da aka samu ta hannun sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar da ke nuna cewa ana amfani da ‘yan sandan da ke aikin samar da tsaro a hukumar wajen cimma wasu ƙudurori da ba aikinsu ba.

Kazalika, sanarwar ta ce akwai buƙatar mutane su fahimci cewa ana tantance ma’aikatan domin martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke watsawa.

A cewar sanarwar matakin ya zama dole domin gyara matsalolin da aka gano game da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta ganin cewa ana amfani da ‘yan sandan da aka tura su samar da tsaro wajen yin kame da gudanar da bincike kan ƙararraki, wanda ƙarara ya nuna cewa sun sauka daga tsarin gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu – wani abu da ya zama dole a yi gyara a kai.

Sannan rundunar  ‘yan sandan ta ce, a baya ma an gudanar da irin wannan aikin tantance ‘yan sandan daga lokacin da aka kafa hukumar a 2015 kuma ‘yan sandan suka koma bakin aiki bayan kammala aikin tantancewar.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya umarci ‘yan sandan da aka gama tantancewa da su gaggauta komawa bakin aiki.