✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwana-kwana daga cikin 19 da suka mutu a wutar dajin Arizona

dan kwana-kwana daga cikin 19 da suka mutu a wutar dajin Arizona ya aike wa matarsa sakon ban kwana Ya turo hoton inda yake zaune,…

dan kwana-kwana daga cikin 19 da suka mutu a wutar dajin Arizona ya aike wa matarsa sakon ban kwana

Ya turo hoton inda yake zaune, da kuma irin launin wutar da ke ci gang-ganga, a daidai inda suke cin abinci,” kamar yadda Juliann ta sanar da kafar yada albarai ta “Today.” Duk da haka musifar ba ta yi muni ba, don haka yana da matukar ban sha’awa mutum ya ga irin wutar da inda yake zaune, a kuma sannan abin da ya sarayar da rayuwarsa a kai, a cewarta.
Juliann ta ce mijinta “mutum ne mai abin mamaki, da na sani a rayuwata.” Ta ce Andrew ya da “wani irin murmushi mai daukar hankali, tamkar zuciyar da aka kawata da zinariya.
Ta yaba wa ’yan kwana-kwana wadanda suka sadaukar da rayuwarsu. “Su gwaraza ne a gidanmu, kuma a cikin al’umma,” ta bayyan wa “Today.” Su gwarazan mutane ne masu taimaka wa al’umma. ’Ya’yanmu za su ci gaba tunawa da su a matsayin gwaraza.”
Jami’an hukuma sun bayyana cewa suna ganin tsawa da guguwa mai karfi da tsananin zafi su suka dabaibaye masu kashe gobarar a cikin wuta.
Shi kuw agwamnan jihar, Jan Brewer a sakon da ya aike ya ce: “Wannan ran ace mummuna da zan iya tunawa da ita. Za a dauki kwanaki masu tsawo kafin bincike ya tabbatar da hakikanin abin da ya auku, amma acikin zuciyarmu mun tabbatar da cewa kashe gobara aiki ne mai hadarin gaske.”