✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan majalisar Kiyawa ya raba kayan abinci na miliyoyin Naira a Dutse

Dan majalisar Kiyawa da Dutse, Alhaji Tijjani Gaya ya raba kayan abinci na kimanin Naira miliyan ashirin da biyar ga al’ummar mazabarsa da nufin agaza…

Dan majalisar Kiyawa da Dutse, Alhaji Tijjani Gaya ya raba kayan abinci na kimanin Naira miliyan ashirin da biyar ga al’ummar mazabarsa da nufin agaza wa marasa karfi da ke yankunan biyu.  Haka nan Alhaji Tijjani ya raba kekunan adaidaita sahu guda 50 da nufin taimaka wa matasa su sami aikin yi tare da saukake rayuwar mata da kananan yara ta hanyar samar da abin hawa don inganta harkokin sufuri a yankuna da lungunan yankin.
Mai magana da yawun matasan, Malam Isma’ila Adamu Fagoji ya shawarci dan majalisar da ya rika bin diddigi wajen ganin irin kayan taimakon al’umma da yake bayarwa suna kaiwa ga wadanda aka yi dominsu, saboda akwai wakilansa da suke makale da yawa daga cikin sakonnin da yake aikawa.   
Da yake karin haske a kan lamarin, Malam Isah Duniya ba-hutu, ya jinjina wa dan majalisar ne tare da yin kira gare shi da ya rika sa ido sosai wajen tabbatar da abin da yake bayarwa na jama’a yana kaiwa gare su.  “Mutane irin Tijjani Kiyawa su ne ya kamata a runguma, amma ba wadanda ba su yi wa kowa komai ba, sai dai su saci kayan jama’a su yi mirsisi.  Muna fata ya ci gaba da gudanar da irin wannan kokari na ganin jama’a sun sami saukin rayuwa”. Inji shi.
Daga nan Malam Isah ya kuma gargadi wadanda aka ba kekunan adaidaita sahun da su yi a hankali wajen kulawa da fasinjojinsu kuma su kauce wa tukin ganganci don su sami amfanin abin, alhalin sun dadada wa jama’ar da suke mu’amala da su.

Gwamnatin Kaduna ta rabar da takin zamani  kyauta ga manoma

  1. Mohammad Yaba, Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ba da umurni ga ma’aikatar noma ta raba takin zamani ga manoman jihar kyauta. A cikin wata kasida da ke dauke da sa hannun babban darakta mai baiwa gwamna shawara a fannin yada labarai, Malam Ahmed Maiyaki, an nun takin zamanin da aka raba kyauta ne ba tare da manoman sun biya ko sisin kwabo ba.
A cewarsa, a kokarin gwamnatin jihar na ganin takin ya isa ga manoma, gwamnatin ta sayi ton dubu sha daya (11,000) domin raba wa manoma da ke mazabu  255 na kananan hukumomin 23 da ke jihar ta Kaduna. “Wannan tallafi da Gwamna Yaro ya baiwa manoma, ya yi hakan ne domin inganta aikin noma a jihar ne baki daya. Kuma akalla ana sa ran manoma 600 ne za su amfana a kowace mazaba.  Sannan kuma za a raba wasu takin ta hanyar kungiyoyin noma 960 da ke a fadin jihar. Kowace mazaba za a ba ta tirelar taki daya na takin  NPK da Urea da SSP da sauran magungunan noma. Gwamnati ta kashe fiye da Naira biliyan daya da rabi (N1.6 bn) a kan sayen takin, wanda kuma duka za a raba musu ne kyauta,” inji shi.