✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Najeriya zai zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Dan Najeriya, Farfesa Tijjani Mohammed Bande ya zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya, inda zai maye gurbin Maria Fermanda Espinosa Garces. Maria Fermanda Espinosa Garces…

Dan Najeriya, Farfesa Tijjani Mohammed Bande ya zama Shugaban Taron Majalisar Dinkin Duniya, inda zai maye gurbin Maria Fermanda Espinosa Garces.

Maria Fermanda Espinosa Garces ce ta bayyana hakan a lokacin da ta kawo ziyara a Fadar Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja.

Shi dai Farfesa Bande shi ne wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya kafin a zabe shi a matsayin wanda zai jagoranci zaman majalisar.

Farfesa Bande haifaffen  garin Zagga ne da ke Jihar Kebbi, kuma ya taba zama shugaban Makarantar Horar da Manayan Ma’aikata wato NIPPS, da ke Kuru a Jihar Filato, sannan kuma tsohon Shugaban Jami’ar Usman Danfodio ne da ke Sakkwato.