✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya harbe abokin aikinsa sannan ya kashe kansa a Abuja

Wani sufeton dan sanda ya bude wa abokan aikinsa wuta mai mukamin Kofur sannan ya raunata wani mataimakin sufeto, wato DSP. A cewar rundunar  ‘yan…

Wani sufeton dan sanda ya bude wa abokan aikinsa wuta mai mukamin Kofur sannan ya raunata wani mataimakin sufeto, wato DSP.

A cewar rundunar  ‘yan sandan Abuja ta ce daga bisani sufeton wanda bata bayyana sunansa ba ya harbe kansa har lahira a ofishin ‘yan sandan da ke unguwar Dutsen Alhaji a Karamar Hukumar Bwari a babban tarayya Abuja.

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan Abuja Bala Ciroma, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na asubahin jiya Lahadi, sannan ya umurci a gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma daukar matakan kare sake aukuwar hakan.