Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dan takarar Gwamnan PDP ya koma APC a Jigawa

Tsohon dan takarar Gwamnan PDP a Jigawa Injiniya Baba Aliyu Santali ya fice daga jam’iyyar ya koma APC, Santali, dai tsohon Kwamishinan ayyuka ne na jihar Jigawa a gwamnatin da ta gabata.

Santali ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP jiya a masaukinsa da ke Kazaure kuma ya ce, ya yanke shawara fita daga jam’iyyar adawa ta PDP don hada kai ga sauran ‘yan Najeriya  wajen sake gina kasa.

ADVERTISEMENT