✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat

Zaune nake a kan kujera a ranar Lahadin da ta gabata ina karanta Jaridar Sunday Trust, sai na ji wayata ta fara kadawa. Da farko…

Zaune nake a kan kujera a ranar Lahadin da ta gabata ina karanta Jaridar Sunday Trust, sai na ji wayata ta fara kadawa. Da farko ban mayar da hankali kan wayar ba saboda dauke mini hankali da labarin da nake karantawa ya yi, sai da wayar ta kusa yankewa sai na yi saurin dauka. Abokina Kabir ne ya kira ni wanda sai a lokacin na tuna mun yi waya da shi a ranar Juma’a har na yi masa alkawarin zan kai masa ziyara.
Bayan na yi gyaran murya sai na ce: “Assalamu alaikum.” Ya amsa cikin fara’a. “Ko ka manta da alkawarin da muka yi ne?” Ya tambaye ni cikin murya mai taushi. Ina sosa keyata alamar ban kyauta ba sai na ce masa: “Yi hakuri gani na zuwa yanzu insha Allahu.” Bayan ya yi dariya sai ya ce: “Sai ka zo, na sanya Hafsat ta yi maka girki na musamman.” Bayan na yi dariyar jin dadi sai na kalli akwatina tare da tunanin tufafin da zan sanya, daga bisani na ce ya gaishe ta kafin na karaso. Daga nan muka yi sallama.
Bayan nan, sai na mike na nufi akwatina sannan na zabi wata jamfa ruwan kasa na sanya, na kuma fesa turare hade sanya hula damanga ita ma ruwan kasa. Daga nan sai na nufi gidan abokina Kabir.
Bayan na isa sai na danna kararrawa, ba tare da bata lokaci ba na ga Hafsat ta fito. Abin ya ba ni mamaki domin ban yi tsammanin ita za ta fito ba, kasancewar duk lokacin da na ziyarce su Kabir ne yake bude mini kofa. Bayan ta gaishe ni a lokacin da nake shiga cikin falon gidan, na kuma amsa ne, sai na tambaye ta ina Kabir kasancewar na duba cikin falon ban gan shi ba, sai ta ce yana bandaki yana yi wa yara wanka. Abin ya ba ni mamaki, na fara tunanin anya Kabir din da na sani ne kuwa? Daga nan ta wuce dakin girka abinci.
Bayan na zauna ina mai ci gaba da tunani ne, sai na ga Kabir ya fito sanye da wando wanda ya kawo masa kwauri da kuma wata singilet baka, cikin sauri bayan mun hada ido ya nufo inda nake. Na mike tsaye, na fadada murmushina, sannan na mika masa hannu, bayan ya miko mini hannu ne ya yi mini kallon ya ji dadin ziyarata. Daga nan muka gaisa, inda na ci gaba da kallonsa cikin mamaki da tunanin sabuwar duniyar da ke zagayawa a gidansa.
Ganin irin yadda nake kallonsa ne sai ya ce: “Kada ka yi mamaki a yanzu rayuwata ta canza. Na shiga wani dausayi mai ni’ima…” Ya yi shiru sakamakon kiransa da Hafsat ta yi, cikin sauri ya nufi dakin girka abinci. Na ci gaba da mamaki, daga nan sai na sake tafiyar da kallona cikin falon, na gan shi tsa-tsaf, ga kamshin turaren wuta na tashi, komai a muhallinsa sabanin lokutan baya da idan na zo nakan gan shi a hargitse kamar dakin mahaukaciya, hakan ya tabbatar mini da zancen da Kabir ya fada mini.
Ana cikin haka sai na ga ya fito da sauri daga dakin girka abinci, sannan ya nufi dakin kwanansu. Bayan wani lokaci ina zaune inda nake ta kalle-kalle sai na ga ya fito goye da Khalid, Humaira kuma na biye da shi. Khalid dan shekara 3 yayin Humaira take da shekara biyar da ‘yan watanni. Bayan sun karaso inda nake ne sai ya ce musu su gaishe da kawunsu, suka gaishe ni cikin ladabi, sannan na rika yi musu wasa tare da tambayarsu me aka koya musu a makaranta. Bayan nan na ce su yi mini ABCD da Alifun, Ba’un, daga nan na ce su je su yi wasa.
Bayan sun fara wasa ne sai na fuskanci Kabir, inda shi kuma ya tattara hankalinsa gare ni, “Yaya na ga dazu ka shiga dakin girka abinci daga nan kuma cikin sauri ka koma dakin kwananku.”
Bayan ya kalli su Khalid sai ya ce: “Na yi wa su Khalid wanka ne sai na manta ban sanya musu kaya ba, shi ne na koma.” Na sake cika da mamaki.
Za mu ci gaba insha Allah.