✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daukar malaman firamare: Sako ga Gwamna El-Rufa’i

Zan so a ba ni fili a  wannan jarida tamu mai albarka da farin jini domin in yi tsokaci  game da yadda Hukumar Ilimi Bai-Daya…

Zan so a ba ni fili a  wannan jarida tamu mai albarka da farin jini domin in yi tsokaci  game da yadda Hukumar Ilimi Bai-Daya (SUBEB) ta Jihar Kaduna ta gudanar da daukar malaman firamare kashi na biyu

Idan masu karatu ba su manta ba a bara ce hukumar bisa izinin Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ta dauki malaman firamare kashi na farko su kimanin dubu 12 bayan an sallami tsofaffin malamai kimanin dubu 22 da ake ganin ba su cancanci koyarwa ba. A wancan lokaci gwamnati ta bayar da sanarwa a kafofin watsa labarai inda ta bukaci duk masu sha’awar koyarwa su nema. Har da tsofaffin malaman da aka sallama ma an ba su dama su nema. 

 

Bayan an yi musu jarrabawa, sai aka sake fitar da wasu sunaye da aka nuna su ne suka yi nasara. Wadanda suka yi nasarar sai aka sake kiransu, inda kafin a ba su takardar daukar aiki sai da aka sake yi musu wasu gwaje-gwaje wadansu ma a gaban Gwamnan aka yi haka. Yin haka ya ba kowa sha’awa, inda kowa ya tabbatar an yi adalci, duk wanda ka ga bai samu ba, to watakila ko dai bai ci jarrabawar ba, ko kuma bayan ya ci jarrabawar amma a wajen sake tantancewar sai aka ga bai cancanta ba, hakan ya sa ba a ba shi takardar daukar aiki ba.

To bayan an gama wannan al’amari, sai bayan wasu watanni, ina ganin a wajejen watan Fabrairu zuwa Maris din bana ne, gwamnatin ta sake bayar da sanarwar za ta sake dibar wadansu malaman firamare kimanin dubu 13 a kashi na biyu.

A wannan lokacin ma gwamnatin ta sanar da ranar da za a rubutu jarrabawar, inda ta bukaci duk mai sha’awa ya nema, ciki har da tsofaffin malaman da aka sallama da wadanda suka rubuta ta farko amma ba su samu nasara ba, su ma za su iya sake nema.  To bayan an gudanar da jarrabawar, sai aka fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da niyyar nan gaba za a sake fitar da wadanda suka yi nasara wadanda ake sa ran su za a ba takardun daukar aiki.

Sai dai an dauki wata da watanni hakan bai samu ba, inda wadansu ma har sun fara cire rai.Wadanda suka yi nasara suna jirar su ji an kira su don a sake ganawa da su wajen tantancewa kamar yadda aka yi a rukunin farko, kwatsam, sai aka ji Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Kaduna Alhaji Nasiru Umar ya shiga gidan rediyo yana cewa ai tuni suka dauki rukunin malamai kashi na biyu, hasali ma har sun ba su takardunsu na daukar aiki bayan an tantance su.

Abin da ya daure wa jama’a kai musamman wadanda suka ga sunayensu bayan sun ci jarrabawar tunda farko shi ne, yaushe aka sake kafe sabon sunayen da aka ce su ne suka yi nasara, kuma a ina?   Shin  a kananan hukumomi aka kafe, ko kuwa a Hukumar SUBEB?  Sannan yaushe ne hukumar ko gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da sanarwar cewa wadanda sunayensu suka fito tunda farko su sake dubawa ko za su dace?

Da ma kafin wannan lokaci, an sha rade-radin cewa ana canja sunayen wadanda suka yi nasara da wadanda suke da uwa a bakin murhu. An yi zargin cewa jami’an da ke kula da daukar malaman suna amfani da wannan dama wajen karbar kudi daga wajen mutanen da ba su ma zauna a jarrabarwar tunda farko ba, amma saboda sun bayar da kudi sai aka sauya sunayensu da na wadanda ke ciki, saboda ba ba su da galihu.  Ke nan sun sayar da damar da wadanda sunayensu suka fito tun farko.

Alal hakika akwai kanshin gaskiya game da wannan zargi.  Don wallahi ina tare da kanwata da ta rubuta jarrabawar sunanta ya fito, kuma tana sauraren ranar da za a sake kiransu ko ta yi nasara ko ba ta yi nasara ba, sai muka ji Shugaban Hukumar SUBEB din a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar da ta wuce a Gidan Rediyon Jihar Kaduna (KSMC) yana cewa ai tuni suka dauki sababbin malamai rukuni na biyu su kimanin dubu 13, kuma za su fara aiki ne daga ranar Litinin da ta gabata (17 ga Satumban nan), kuma tuni aka tura su makarantun da za su koyar.

Wannan abu ya daure mata kai da ire-irenta wadanda abin ya zo musu tamkar mafarki.

Rokon da muke yi wa Gwamna El-Rufa’i shi ne, ya kamata ya kafa kwamitin bincike game da yadda hukumar ta dauki wadannan sababbin malamai a karo na biyu, saboda a gaskiya akwai cuwa-cuwa a ciki.

Jama’a sun dauka cewa gwamnatin Jihar Kaduna tana yaki da cin hanci da almundahana, amma sai ga shi ana aikata irin wadannan abubuwa na zalunci da danniya.

Na tabbatar akwai da yawa daga cikin masu irin wannan korafi amma saboda ba su da yadda za su yi, ta sa suka yi shiru.

Idan Gwamnan yana tababa, to don girman Allah ya yi hira da kowane gidan rediyo na Jihar Kaduna sannan ya ba jama’a dama su kira shi kai-tsaye don su yi masa tambayoyi ko su yi masa bayani game da yadda daukar malaman firamaren ya gudana a karo na biyu.  Hakan zai tabbatar masa da cewa gaskiya na fada ko karya na yi.

Idan bai yi haka ba, to jama’a za su dauka dama batun da yake yi na yaki da cin hanci da danniya a baki ne kawai ba a aikace ba.

 

Sannan Shugaban Hukumar SUBEB din ya kara da cewa, yanzu haka daliban firamaren da ke cikin kowane aji ba su wuce 40 ba. To a nan ma ina da ja, domin maganar gaskiya ban san firamaren da ke da dalibai kasa da 100 a kowane aji a halin da ake ciki ba. Misali daliban makarantar firamaren da nake makwabtaka da ita wato L.E.A Primary School Fulani Road, Tudun Wada, Kaduna a kowane aji akan samu dalibai fiye da 100. 

 

In har da gaske akwai firamaren da dalibai ba su wuce 40 a kowane aji ba, to ina kalubalanr Malam Nasiru Umar ya sanar mu kuma za mu yi bincike kuma insha Allahu za mu yi masa adalci wajen sanar da duniya halin da ake ciki.

Ta ina yara za su samu ingantaccen ilimi a irin wannan yanayi?

A karshe ina fata na kusa da Mai girma Gwamna shi za su isar masa da wannan wasika don ya dube ta da idon rahama kuma ya yi bincike game da korafin da muke yi na daukar malaman firamare a Jihar Kaduna ba bisa ka’ida ba.

 

Na gode. 

 

Allah Ya taimaki Najeriya da Jihar Kaduna, amin.

 

Muhammad Sani Shokin, 08097015805