✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dodonniya ta addabi mutanen Gashuwa

Wata Dodonniya mai kama da Kura da ke awon gaba da tumakin al`ummar garin Gashuwa ta Jihar Yobe ta hana samari unguwannin daban-daban barci a…

Wata Dodonniya mai kama da Kura da ke awon gaba da tumakin al`ummar garin Gashuwa ta Jihar Yobe ta hana samari unguwannin daban-daban barci a cikin dare domin kubuta daga sharrinta.
Unguwanni da abun ya shafa sun hada da Kabalar kara da Fulatari da Sabon layi da Garin lamido da kuma Gobernment lodge. Rahotanni sun tabbatar da ta hallaka raguna da tunkiyoyi masu dimbin yawa a cikin makonni biyu da suka shude.
Aminiya ta rawaito cewa, samarin sun kudiri aniyar hana idanuwansu barci ne domin kawo karshen ta`asar da wannan Dodonniya take yi a gidajen al`ummar wadannan ungwannin, tare kuma da tsoron kar ta fara kashe mutane  
Sai dai kuma kakakin rundunar `Yansanda ta Jihar Yobe, ASP Toyin Gbadegesin ya ce har lokacin da wakilinmu ya tuntube shi ba su  samu wani koke daga  al`ummar yankin ba, “Na tuntubi DPO mai kula da yankin amma ya ce ba su da wannan labarin, kuma ba a kai musu rahota ba. Saboda haka mu ke tunanin watakila camfi ne ko jita-jitar mutane garin.”
Malam Umar Kabala, daya ne daga cikin samarin da ke sintirin gadin unguwannin, ya tabbatar wa wakilinmu cewa sun yi arangama da Dodonni biyu a cikin daren ranar  Litinin din makon jiya sakamakon fakonta da sukayi a unguwar Kabalar Kara. “Da mutanen unguwannin suka ga lamarin Dodonniyar na nema ya ta`azara, sai mu samari muka sha alwashin hana idanunmu barci domin ganin mun magance matsalar. Saboda akwai fargabar kar ta`addancin Dodonniyar ya tsallake dabbobi zuwa ga iyalanmu da sauran bani-Adam.’’
“Da dare, misalin karfe 12:45 sai muka rarraba matasa majiya karfi kashi-kashi a cikin unguwannin, wasu a kan bishiyoyi, wasu kan shigifa, domin yin fakonta. Kowannenmu yana rike da mabugi da fitilar hannu; can cikin sulisin dare sai muka hangi wadansu hallitu guda biyu suna tunkaro unguwar. Wani daga cikinmu sai ya yi gajen hakuri ya haska musu idanu, wanda haka ya sa suka juya a guje mu kuma bi ba. Har sai da muka rutsa su a wani lungu da ba ya fita, amman suka bata. ”
Umar ya misilta wadannan dodonni da halittu masu rikida a lokacin da suke biye da su, haka kuma ya kara da cewar, “Da farko suna kama da kura, amma da muka cigaba da binsu sai suka rikida zuwa surar mutane kafin suka bata.’’
Ya ce, kuma abin mamaki, hatta karnuka da suka gansu rugawa cikin gida suka yi. “kafafunsu hudu ne, da dagi irin na kura, amma yatsunsu na mutune ne. Babban abin mamakin shi ne yadda suka yi batan-dabo da muka rutsa su a wani gidan kara.”
Malam Sa’idu Zakiru, mai gadin Ma`aikatar filaye ta jihar Yobe, na daya daga cikin wadanda dodonniyar  ta cinye wa tunkiya, ya ce,“Ina wajen gadi sai mai dakina ta zo a guje ta ce, `rugo kare zai cinye maka tunkiya.` Isa ta ke da wuya sai na tarar da tunkiyar a kwance, an fede fatar wuyanta an ajiye ta a gefe. Babban abin al`ajabin shi ne, babu alamun jini a wuyan tunkiyar, amma an kwakule tsokar wuyan. Jini bai zuba a wuyan dabbar nan ba har sai da na yanka da wuka. Matata ta ce ba ta ga abun da idonta ba, saboda da Dodonniyar  ta ji karar bude dakin sai ta gudu, amma mutane sun ce kambultu ne. Naira dubu sha daya (N11,000) na siyo tunkiyar domin in yanka ranar sunan danmu, amma da na kai ta mahautan Naira dubu hudu suka saya.”
Ya kuma kara da cewa, Dodonniyar ta shiga gidan makwabcinsa a Unguwar Sabon-gari da misalin karfe daya na dare, inda ka kwakule kayan cikin Raguna biyu. “A nan ma sun ce babu alamun jini. Sa’annan sai da ta fede fatar ragunan kafin ta zare hanjin, ta cinye hantar da huhun ragunan.”  
Malam Awana Mhammad, majin matar da Dodonniyar  ta shiga gidanta ne, ya ce Dodonniyar  ba ta shiga gida sai ta tabbatar mai gidan ba ya nan. “Abin mamaki, duk gidajen da ta shiga mazajensu ba sa nan. Wani lokaci ta tsoratar da matan gidan idan sun fito fitsari, sa’anan ta yi awon gaba da dabbobinsu. Ta shiga gidan Ussani mai Garaya da Malam Haruna Gada, kuma dukkansu ba sa gari. Wannan kuma shi ya sa muka yi tunanin  kar ta fara kashe mutane.”
“Haka nan kuma rago da tunkiya kosassu kadai take ci , ba ta cin akuya ko kaji. Wannan shi ya sa mutane da dama ke zargin cewa wadansu matsafa ne da ke cikin al`umma ke rikida su aikata wannan ta`adi. Saboda a tsawon rayuwata ban taba ganin ko jin labarin dabbar da za ta tsotse jinin dabba ba tare da an ga shaida ba. Amma wannan ba za ka taba ganin jini ko digo ba.”
Malama Jimmala, matar Awana ta bayyana wa Aminiya cewa, Dodonniyar ta shiga gidansu ne a ungwar Kabala Kara, kimanin karfe daya da rabi (1:30) na dare, ta dauke mata tunkiya wadda daga bisani aka tarar da gawarta a kofar gida.
“Muna kwance a daki da misalin 1:30 zuwa 2:00 sai muka ji buruntu a waje, to da yake mun dan tsorata ba mu fito ba, shiru har gari ya waye, shi ne sai muka ga babu tunkiyarmu. A da mun yi  zargin cewa barawo ne ya ziyarce mu, amma abin mamaki sai muka tarar da ita jefe a kofar gida, an kwashe kayan cikinta. Sannan wani abin mamaki, babu alamar jini ya zuba. Wannan al`amari ya tsoratar da mu har muke tunanin barin unguwar.” Inji Malamar.
Mutanen unguwannin da abin ya faru duk sun tabbatar da faruwar al`amarin, tare kuma da gabatar da hujjoji, amma akwai sabanin ra`ayoyi dangane da kammanin wannan Dodonniya, domin wadansu daga suna misalta Dodonniyar  da Kura mara bindi, wadansu da farin kare, wadansu kuma da kanbultu, amma dukkansu sun tabbatar da cewa tana rikida ta zama mutum idan har aka kure mata, kafin ta bata.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban bangaren lafiyar Dabbobi na Ma’aikatar Kula da Bunkasar Dabbobin Jihar Yobe, Dokta Idris Yusuf Madaki, ya bayyana shakkun cewa Dodonniya ke aikata wannan ta’asar
Ya ce,a bisa binciken da suka gudanar a cikin makon da ya shude, sun gano cewa kare ne da ya rika ko Dila su ke aiwatar ta wannan barnar. “Ma’aikatanmu da  ke Gashuwa da suka dauki wasu daga cikin dabbobin da aka ji wa ciwo ba su mutu ba su ka yi musu magani, sun tabbatar mani cewa kare ne da ya rika ko kuma naman daji irinsu Dila ke yin wannan barnar.  Abin da ya sa muka fi zargin Dila ne,  shi ne, ba zai taba yarda a ganshi ba. Sa’annan kuma kisan da ake yi wa dabbobin yanayin farautarsa ne.”
Hakan kuma ya kara da cewa, a kimiyance ba su yarda akwai wani abu Dodo ba, “Kuma mutanen duk da muka tambaya sun kwatanta shi ne da kare ko kura. Wanda haka ya sa muka amintu da cewa dayan biyunsu ne, amma ba Dodo ba.”
Dangane da ko za a iya cin naman dabbar da aka ji wa ciwon, sai ya ce,”Wannan amsar na da wahalar bayarwa, na daya dai za mu kalle ta ta fuska biyu: a addinace da kuma kimiyance. A kimiyance ba za a ci ba saboda ba a san me ya ji mata ciwo ko ya kashe ta ba. Tana iya yiyuwa yana dauke da wata cutar da cin naman ka iya harbin mutane.’’
“A Addinance kuma sai malamai su yi bayani, saboda ba karen farauta ne ya kashe dabbar ba. Sai dai Malamai sun yi tambohi a takaice.”