✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Hana Fita: ’Yan sanda sun kashe matasa hudu a Kaduna

Wasu matasa hudu sun rasa rayukansu a sakamakon harbinsu da ’yan sanda suka yi saboda kin bin dokar zama a gida. Lamarin ya faru ne…

Wasu matasa hudu sun rasa rayukansu a sakamakon harbinsu da ’yan sanda suka yi saboda kin bin dokar zama a gida.

Lamarin ya faru ne a unguwar Tirkaniya  da ke cikin garin Kaduna a ranar Litinin din nan da ta gabata.

Daya daga cikin Shugabannin unguwar Kwamred Nuhu Muhammad Marafan Nasarawa, ya tabbatar da cewa sun binne wadanda suka rasa rayukansu.

An ce matasan sun fara rikicin ne da jami’an JTF wadanda suka yi kokarin hana su sayan kayan abinci a kusa da titin jirgi da ke a Unguwar, kafin daga bisani ’yan sanda suka shigo suka bude wuta.

Ya kara da cewa, akwai mutum goma da suka samu raunuka ‎bakwai na cikin rai fakwai mutu fakwai a wani asibiti da aka sakaya sunansa.

” Mun binne mutum hudu da suka rasu akwai sauran mutum goma da suka samu raunuka sannan bakwai daga cikinsu na kwance cikin wani hali.” In ji shi.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar Muhammad Jalige, ya ce suna jira su ji daga bakin jami’in ’yan sandan yankin kafin su fitar da ta su sanarwar.