✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dokar hana shiga da kaya za ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya’

Sarkin Hausawan Kwatano a Kasar Benin, Ambasadan Zama Lafiya a Afirka, Dokta Mahammadu Mouniru Garba Nakura wanda shi ne Matainmakin Shugaban ‘Yan Najeriya mazauna Kasar…

Sarkin Hausawan Kwatano a Kasar Benin, Ambasadan Zama Lafiya a Afirka, Dokta Mahammadu Mouniru Garba Nakura wanda shi ne Matainmakin Shugaban ‘Yan Najeriya mazauna Kasar Benin, ya shaida wa Aminiya ra’ayinsa a kan harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna da kuma siyasa a Najeriya. Ga yadda tattauwar ta kasance:

Aminiya: Me za ka ce a kan dokar hana shiga da kaya ta kan iyakoki da Najeriya ta yi?

Tabbas wannan doka ce da zata yi amfani wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya a nan gaba. Ka sani cewa bunkasar arzikin Najeriya shi ne bunkasar arzikin Kasar Benin da wasu kasashen Afirka ta Yamma domin sun dogara da Najeriya ne ta wasu fannoni. Amma da gangan wasu mutane suke amfani da siyasa wajen sukar wannan doka suna bata sunan Shugaba Muhammadu Buhari alhali kowa ya sani ba laifinsa ba ne. A matsayinmu na ‘yan Najeriya dake hada-hadar kasuwanci a nan Kasar Benin muna jinjinawa Gwamnatin Najeriya a kan tsaurara matakan tsaro da sanya ido a kan iyakokin Kasa da Kasa domin hana shiga da wasu kaya cikin Najeriya daga Kasashen Turai.

Aminiya: Ko wannan doka ta shafi harkokin kasuwancinku a kasar Benin?

Kwarai kuwa domin harkokin kasuwancinmu na kasa da kasa sun durkushe sun tsaya cik daga lokacin da wannan doka ta fara aiki. A matsayinmu na ‘yan kasuwa bamu taba shiga cikin mawuyacin halin kasuwanci kamar wannan lokaci ba. Ita kanta Gwamnatin Benin tana cikin damuwa a yanzu a dalilin kafa wannan doka domin da yawa daga cikin kudaden shigarta suna fitowa ne daga irin kayan da ake safararsu daga kasashen duniya ana ratsawa ta cikin kasar Benin domin shiga da su Najeriya. Amma wallahi duk da wannan mawuyacin hali da muke ciki a dalilin kafa dokar bamu damu ba, domin mun san cewa za mu ci amfaninta a nan gaba.

Aminiya: A matsayinka na dan kasuwa ko akwai matsala tsakaninku da jami’an tsaron Najeriya da Benin ta fannin shiga da fitar da kaya a kan iyakoki?

Akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu da jami’an tsaron wadannan kasashe biyu musamman a kan iyakar Seme da sauran iyakokin kasa da kasa saboda muna biyan harajin fito domin girmama dokokin kasashen biyu wajen shiga ko fitar da kayanmu. Kuma kungiyarmu ta ‘yan Najeriya mazauna kasar Benin, Nigerians in Diaspora Organisation (NIDO) tana yin iya kokarin ganin ta shawo kan dukkan wata matsala a tsakanin kowane dan Najeriya da jami’an tsaro a kan iyakoki ko a cikin kasar da muke zaune.

Aminiya: Ya ya batun zamantakewar al’ummarka Hausawa da mutanen garin Kwatano?

Babu wata matsala tsakaninmu da mutanen kasar Benin domin akwai auratayya a tsakani. Kuma mutanenmu da dukkan ‘yan Najeriya dake zaune a wannan kasa suna samun ‘yanci da yake kai su ga tsayawa takarar mukaman majalisun kasa.

Aminiya: A yanzu ya kake kallon siyasa a kasarka Najeriya?

To mu dai ba ‘yan siyasa ba ne amma a duk lokacin da babban zabe ya gabato muna komawa garuruwanmu a Najeriya domin zabar mutanen da muke so su shugabanci kasar. Muhimmin abun da zan iya cewa a game da siyasar Najeriya a yanzu shi ne, shawara ce nake ba ‘yan Najeriya don Allah mu yi hakuri da juna mu yi siyasa ba da gaba ba, mu yi watsi da siyasar kabilanci da bambancin addini, mu nuna kishin kasarmu a idon duniya. Sannan kuma ina rokon ‘yin Najeriya baki daya su fuskanci irin yadda duniya take canza salo da yadda muka tsinci kanmu a yanzu mu kyale wannan dattijo Shugaba Muhammadu Buhari ya karasa zango na biyu na shugabancin kasa domin yin haka ne zai ba shi damar kammala muhimman ayyukan ci gaba da ya fara shekaru uku da wucewa. Irin wadannan muhimman ayyuka sun hada da matsalar Boko Haram da tsagerun Neja Delta da masu fafutukar ballewa domin kafa kasar Biyafara.

Aminiya: Ka yi magana ne kawai a kan tsaro, babu wani abu da kake ganin ita gwamnatin Najeriya ta yi wanda ya isa a jinjina mata?

Ina ganin tsaron kasa shi ne a kan gaba domin idan babu tsaro to kuwa babu harkar da za ta gudana. Duk da haka ina so ka waiwaya baya ka ga yadda aka dakile harkokin cin hanci da rashawa wanda kasashen duniya suka jinjina wa Najeriya a kan haka kuma suka dawo mata da dimbin kudaden da aka sace aka ajiye a cikin bankunansu. Kuma ga batun bunkasa harkokin noma da matsalar karancin wutar lantarki ka ji shiru an daina korafi a kai sannan ga batun manyan hanyoyin kasa da aka bayar da kwangilar sake gina su tare da samar da ayyuka ga miliyoyin matasa da sauransu.