✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar kulle: Masari ya sassauta bayan ya gana da malaman addini

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayar da umarnin sassauta dokar kulle na tsawon mako guda a jihar.Sakataren gwamnatin jihar ta Katsina, Mustapha Inuwa,…

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayar da umarnin sassauta dokar kulle na tsawon mako guda a jihar.Sakataren gwamnatin jihar ta Katsina, Mustapha Inuwa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Mustapha Inuwa ya ce gwamnati ta yanke shawarar sassauta dokar ne bayan ganawarta da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar yayin taron da ta saba gudanarwa.

Ya kara da cewa sassauta dokar kullen za ta fara aiki ne daga ranar Litinin zuwa Lahadi, 18 zuwa 24 ga watan Mayu.

Ya ce za a sassauta dokar ne a cikin kananan hukumomin jihar, amma  dokar hana shige da fice a tsakanin kananan hukumomin jihar na nan kamar yadda take a baya.

Sanarwar ta  bayyana cewa Gwamna Aminu  Masari ya umarci Sarkin Daura da Sarkin Katsina da sauran manyan masu rike da sarautar gargajiya a kan su tabbatar da cewa dagatai sun zauna a garuruwansu tare da jama’arsu yayin bukukuwan Sallah.

Sakataren gwamnatin ya bukaci al’ummar jihar da su kiyaye dokar hana yaduwar coronavirus, inda ya shawarci masu yawan shekaru da marasa lafiya su guji shiga taron jama’a.

A ranar 20 ga watan Afrilu gwamnatin jihar Katsina ta kafa dokar kulle a birnin Katsina, bayan an kafa dokar a garin Daura da karamar hukumar Dutsinma.