Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dora wa ‘yan siyasa bukatu da jama’a ke yi na ta’azzara cin hanci da rashawa – Kungiyar CICILAC

Wadansu daga cikin mahalartar taron da Qungiyar CICILAC ta gudanar
Wadansu daga cikin mahalartar taron da Qungiyar CICILAC ta gudanar

An bayyana cewa neman biyan bukatun kashin kai da jama’a ke yi daga masu rike da mukaman siyasa yana ta’azzara harkar cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.

Wani jami’i a Sashen Ilimantarwa a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC), Sufirtanda Dalhatu Abdullahi ne ya bayyana haka a wajen taron wayar da kai kan yaki da cin hanci da rashawa da Kungiyar Kula da Ayyukan ’Yan Majalisa (CICILAC) ta shirya a Kano.

ADVERTISEMENT

Sufiritanda Dalhatu ya bayyana cewa shugabanni sukan yi duk me yiyuwa don ganin sun biya wa jama’a bukatu gudun kada su ki zabensu a nan gaba. “Yawancin lokaci mutane na damun shugabanni da bukatu na kashin kai inda wani zai je ya nemi kudin makarantar ’ya’yansa wadansu kuma kudin magani. Su kuma don gudun kada a ki zabensu nan gaba sai su shiga harkar cin hanci da rashawa su debi kudin da ya kamata a yi wa al’umma aiki su raba wa jama’ar,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Ya kamata jama’a su fahimci cewa ofisoshin gwamnati ba wuri ne na samun kudi ba, wuri ne na aiki ga jama’a da gina kasa.”

ADVERTISEMENT

Tun farko a jawabin Jami’a a Kungiyar CICILAC, Misis Bathsheba Tagwai ta ce kungiyar ta shirya taron ne da nufin wayar da kan jama’a a kan damar da suke da ita ta tona asirin duk wani abu da suka ga ana yi da ya shafi cin hanci da rashawa inda su kuma za su tura shi ga hukumomin da suka dace, “Don muna da fahimtar juna a tsakaninmu da hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da ke fadin kasar nan har ma da ta  duniya  wato  Transparency  International. Kungiyar CICILAC ta samar da cibiya ta musamman da take yi wa take da ALAC don sauraren korafe-korafen al’umma wadda ita kuma za ta tura abin ga hukumar da ta dace tare da bibiyar lamarin har sai ta ga an hukunta mai laifi,” inji ta.

Kungiyar CICILAC ta ba jama’a tabbacin samun kariya game da rahoton da suka yi, matukar suna da hujjoji masu karfi a kan rahoton da suka bayar

A jawabin Babban Jami’i a Cibiyar CITAD, Isah Garba, ya ce akwai bukatar al’umma ta rika bibiyar ma’aikatun gwamnati don samun bayanai kan yadda ake kashe kasafin kudin hukumomi, domin hakan zai dakile cin hanci da rashawa a hukumomin gwamnati. “Doka ta ba jama’a damar neman bayanai daga ma’aikatun gwamnati game da yadda suke kashe kudadensu haka kuma ta tilasta jami’an su bayar da dukan bayanan da ake nema. Idan har mutane suna bibiyar hakan zai sanya ma’ikata su rika taka-tsantsa da dukiyar al’umma wanda kuma zai dakile cin hanci da rashawa,” inii shi.