Da Dumi Dumi

Dorayi da Sheshe sun haska a wurin karrama ’yan fim na Afirka taYamma

A ranar 22 ga Disamban nan ne aka yi bikin karrama mawaka da ’yan fim na yankin Afirka ta Yamma mai suna West African Music and Mobie Awards 2019 karo na 6 a dakin taro na Marhaba da ke birnin Kano.

A taron, Falalu Dorayi ne ya lashe kyautar Gwarzon Jarumi da fim din Fuska Biyu, sai TY Shaba ya lashe kyautar karamin jarumi da fim din Nisan Dare.

Fim din Barazana, wanda TY Shaba ya dauki nauyi ya lashe kyaututtuka uku da suka hada da kyautar kwalliya da tacewa (editing).

Fim din Takaddama wanda Alhaji Sheshe ya dauki ya samu kyautar bin tsarin fim.

Da yake jawabi kan bikin, TY Shaba ya ce an samu nasarori da dama, kuma an samu wasu kalubabale da za a gyara.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, “Daga cikin nasarori da aka samu, akwai kullar alakar aiki a tsakanin ’yan fim na Afirka ta Yamma, kuma Gwamnatin Nijar da ’yan kasuwar kasar sun bayar da gudunmawa mai yawa.

Haka an karrama mawaka da ’yan fim 67, kuma kowanne ya kai kimanin Naira dubu 100 a daraja.”

Da ya juya kan kalubalen da aka samu, ya ce an yi garaje wajen sauya wa bikin suna daga bikin karrama mawaka da ’yan fim na Arewa (Arewa Music and Mobie Awards- AMMA) zuwa na Afirka ta Yamma, West African Music and Mobie Awards (WAMMA), sai ya bayyana yadda ba a samu gudunmawa daga Gwamnatin Jihar Kano ba da rashin halartar wadansu daga cikin manyan masu ruwa-da-tsaki na Kannywood a matsayin wasu kalubale.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya