Da Dumi Dumi

Dubi kan nazarin Hausa da Hausa (I)

Asalin Hausa (1)

Tun lokacin da Turawa suka fito da tsarin nazarin harshen Hausa suka sanya ana yin nazarin a cikin harshen Ingilshi tare da Hausa gaba daya.

Sun yi haka ne domin su ne suke yin nazarin harshen a farkon lokaci saboda su ji dadin mulki a kasar Hausa, inda suka yi nazarin harshen sosai, suka binciki komai da komai da ya shafi rayuwar Malam Bahaushe. Shi ya sanya aka dauki lokaci mai tsawo saboda Turawa ne suke da manyan shehunan malamai a harshen Hausa,  duk wani dan Afirka wanda yake bukatar samun  digiri na uku sai ya tafi Ingila, saboda karancin malaman da za su duba shi a cikin gida Najeriya da kewayenta.

Amma yanzu manazarta harshen Hausa sun yawaita, ta yadda a yanzu ba sai an tafi kasar waje ba za a iya samun digiri kowane iri har zuwa matakin Farfesa, domin akwai shehunnan malamai a wannan fanni a kwalejoji da jami’o’in da ke Najeriya da makwabtanta.

Har Turawan mulkin mallaka suka bar kasar nan ana ci gaba da nazarin harshen Hausa da Ingilishi ne, shi ya sanya duk wanda ya karanta harshen Hausa idan yana magana da Ingilishi sai a yi tunanin ko Ingilishin ne zalla ya karanta.

Amma a farkon shekarun 1980 sai aka yanke shawarar a rika koyar da Hausa da harshen Hausa zalla, hakan ya sanya aka koma ana nazarin Nahawun Hausa tun daga kwayar sauti har zuwa jimla da harshen Hausa, haka a fannin adabi da ya kushi wakoki da zube da wasan kwaikwayo da sauran fannoni na harshen Hausa.

ADVERTISEMENT

Wadanda suka yi wannan tunanin sun yi haka ne da kyakkyawar niyya saboda tsananin kishin Hausa da suke da shi, wanda ya sanya ba su so a danganta harshen Hausa da Turancin Ingilishi ko Turancin Faranshi.

Sai dai kuma maimakon hakan ya kara daukaka matsayin daliban ilimin harshen Hausa, musamman Hausawa da ke nazarin harshen, sai hakan ya zama matsala a gare su, domin Turawan Ingila da suka mulki Najeriya sun kakaba wa kasar harshen Ingilishi ne a matsayin harshen kasa, wato harshen da hukuma take hulda da shi. Shi ya sanya Shugaba ko Bahaushe ne idan yana jawabi ga ’yan uwansa Hausawa a hukumance sai ya yi magana da Ingilishi sannan daga bisani ya fassara ko wani ya fassara abin da ta fada da Hausa.

Wannan ya sanya dole duk mai nazarin harshen Hausa sai ya fahimci harshen Ingilishi sosai saboda ya rika yin fassara mai kyau ba kassara ba, domin babu yadda za a yi fassara ingantacciya ta samu sai mai fassarar ya fahimci harsunan guda biyu sosai, wato da harshen asali da harshen karba.

Sai dai kuma a ganina kamar an yi gaggawa wajen soke nazarin Hausa da ake yi da Ingilishi aka koma Hausa zalla, domin kuwa saboda da karancin ilimi a harshen Ingilishi ne ya sanya a halin yanzu ake yawan samun matsala a wajen fassara daga Ingilishi zuwa Hausa ko daga Hausa zuwa Ingilishi.

Wannan ne ya sanya ake samun wadanda suka karanta Hausa a matakin digiri suke yin gurguwar fassara a wuraren da suke gudanar da ayyukansu, sai ya kasance wadanda ba su karanta Hausar zalla ba, kamar wadanda suka karanta fannin aikin jarida ko suka karanta Hausa tare da wani darasi daban ko wadanda suka karanta Hausa a matakin share fagen shiga jami’a amma suka karanta wani fannin daban, sun fi iya fassara saboda Ingilishinsu yana da kwari. Shi ya sanya yanzu a kafofin yada labarai da dama da ake amfani da harshen Hausa ba wadanda suka karanta harshen Hausa ba ne suka mamaye su.

Kafin wannan lokacin wanda ya karanta Hausa yana iya aiki a ko’ina ba tare da shakkar komai ba domin duk abin da wanda ya karanta Ingilishi zai yi shi ma zai iya, har ma yana iya fin sa saboda shi harsuna guda biyu ya kware a kansu. Amma yanzu wadansu daliban da suka karanta Hausa tsoron shiga wurin da ake amfani da Ingilishi zalla suke yi saboda suna da matsala wajen yin magana da harshen Ingilishi.

Mu kwana nan.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya