✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk mai zargin na ci kudi kada ya rufa min asiri – Yari

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari, ya ce duk wanda ya san cewa ya yi sata, ko rub-da-ciki a kan dukiyar jama’a , to…

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari, ya ce duk wanda ya san cewa ya yi sata, ko rub-da-ciki a kan dukiyar jama’a , to don Allah ya zo ya tona masa asiri.

Alhaji Abdul’aziz Yari, ya ce ko ma wane ne, to ya kawo hujja kwakkwara da za ta gamsar da hukuma, har a hukunta shi.

Alhaji Yari ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadin da ta gabata, a gidansa da ke garin Talatar Mafara a Jihar Zamfara.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakunci shugabannin Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara.

Ya ce, “Duk wanda ya ce na kwashi dukiyar gwamnati na boye walau a nan a kasar ko wajen Najeriya, ya fito da hujja ya tona min asiri. “A matsayina na Gwamna, aikina shi ne kashe kudade, kuma abin da na yi ke nan, amma a bisa ka’idar ciyar da Jihar Zamfara gaba, da kuma amfanar al’ummar Jihar Zamfara,” inji shi.

Ya ce “Na yi imani, kuma na san cewa duk abin da ya same ni, to kaddara ce daga Allah. Don haka masu ganin cewa za su iya narkar da ni, ko su karya ni, ko su dankwafar da ni, to ba za su samu nasara ba.”

Yari ya isa gida Talata Mafara ne bayan ya dawo daga Aikin Hajjin bana. Kuma ya isa tare da jami’an tsaro masu yi masa rakiya, tun daga filin jiragen sama na Sakkwato.

A gida kuma dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC suka fito taryarsa daga dukkan kananan hukumomin jihar, ciki kuwa har da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Alhaji Lawal Liman.