✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk wanda ya mutu yana aikin kare kasarsa ya yi shahada – Sheikh Namadi

Limamin Masallacin Juma’a na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunna na garin Sabo Abeokuta, kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar a Jihar Ogun,  Sheikh…

Limamin Masallacin Juma’a na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunna na garin Sabo Abeokuta, kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar a Jihar Ogun,  Sheikh Muhammadu Namadi, ya bayyana cewa, duk mutumin da ya rasa ransa a lokacin da yake kare kasarsa ya yi shahada. Ya ce fadin Manzon Allah (SAW)  ne domin “Manzon Allah ne ya fadi hakan ya ce, da wanda ya rasa ransa a kan kare kasarsa da wanda ya rasa ransa a kan kare iyalansa da wanda ya rasa ransa a lokacin da yake kokarin kare dukiyarsa ya yi shahada, duk wanda ya mutu a kan wadannan abubuwa uku, ya yi shahada,” inji Ustaz Muhammadu Namadi a lokacin da ya jagoranci jana’izar jami’in hukumar Kwastam Yakubu Shu’aibu Pindiga wanda ’yan fasakwauri suka kashe a Jihar Ogun.

Bayan da sheihin malamin ya jagoranci yi wa marigayin jana’iza, jim kadan da binne shi a makabartar garin Sabo Abeokuta, malamin ya yi wa jama’ar da suka yi rakiyar gawar nasiha, ya ce duk wanda ya mutu a kan kare kasarsa ya yi shahada, “Don haka mu kyautata zato cewa wannan bawan Allah ma’aikacin Kwastam da muka binne ya yi shahada domin ya mutu ne a kan kare kasarsa, zan kuma mu yi amfani da wannan dama na yin kira ga abokan aikinsa da kada su manta da shi, su rika yi masa addu’a kana a kula da hakkinsa. Don haka ina kira ga mahukunta da su rika kula da hakkin jami’ansu da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aiki, wannan bawan Allah da ya rasu ya bar ’ya’ya da mata, to kamata ya yi a ba su kulawa ta musanman, hakan shi zai bai wa abokan aikinsa wadanda suke raye kwarin gwiwa,” inji shi.

Ya ce, duk mai rai mamaci ne kowa sai ya dandani mutuwa ko a kusa ko a nesa. “Don haka kamata ya yi a kowane lokaci mu kasance cikin shirin gamuwa da Allah domin babu wanda ya san lokacin da mutuwa za ta riske shi. Saboda haka mai hankali shi ke tanadin mutuwa a kowane lokaci ta fuskar yin ayyuka nagari tare da kyautata dabi’u da mu’amala. Gatan mamaci uku ne da zarar ya mutu, biyu daga ciki za su rako shi bakin kabari kuma guda daya ne zai zauna tare da shi. Idan mutum ya mutu jama’arsa da dukiyarsa ko matsayinsa za su rako shi bakin kabarinsa, wannan jama’a da dukiyar za su koma su juya bayan an binne shi. Aikin da ya rika yi kadai zai bi shi har kabarinsa. Gatan da ake fara yi wa mutum bayan an binne shi shi ne a bincika a ji wa ke bin sa bashi, sai an biya masa basusukkansa kaf sannan a taba gadonsa,” inji shi.

Al’ummar garin Sabo Abeokuta, sun cika da alhini sakamakon kisan jami’in Kwastam din wanda ’yan fasakwauri suka bude musu wuta a ranar Asabar din da ta wuce a kan hanyar Idiroko lokacin da suka kama wata shinkafar fasakwauri suna kan hanyar tafiya da ita. Lamarin ya jawo jikkata jami’an Kwastam biyu wadanda aka kai su Cibiyar Lafiya  ta Tarayya da ke Abeokuta inda Yakubu Shu’aibu Pindiga, ya rasu bayan kwana guda sakamakon raunin harbin da aka yi masa kuma an yi jana’izarsa da yammacin ranar Lahadin da ta gabata a garin Sabo Abeokuta.

Marigayin dan Jihar Gombe, kafin rasuwarsa jami’in Hukumar Kwastam ne mai anini biyu da ke aiki da Hukumar ta FOU shiyya ta daya a Legas, ya rasu ya bar matar aure da ’ya’ya biyu. Abokansa musamman daga Jihar Gombe sun yi ta sanya hotunansa a kafafen sada zumunta tare da yi masa addu’ar samun rahama.

Mai magana da yawun Hukumar Kwastam ta FOU a Legas Jerry Attah, ya shaida wa Aminiya cewa, suna kan bincike don gano ’yan fasakwaurin da suka yi aika-aikar

A watan Janairun da ya gabata, ’yan fasakwauri a Jihar Ogun sun hallaka wani jami’in Hukumar Kwastam mai suna Hamisu wanda shi ma aka binne shi a garin Sabo Abeokuta.