✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duke ya nuna damuwarsa a kan koma bayan Arewa

Dan takarar Shugaban Kasa karkashin SDP, Dokta Donald Duke ya nuna damuwarsa game da irin koma bayan da Arewacin Najeriya yake ciki, duba da cewar…

Dan takarar Shugaban Kasa karkashin SDP, Dokta Donald Duke ya nuna damuwarsa game da irin koma bayan da Arewacin Najeriya yake ciki, duba da cewar Arewa ita ce mafi yawan jama’a a Najeriya sannan ita ce kan gaba wajan ma’adanai.

Donald Duke ya fadi haka ne a ranar Asabar na makon jiya, a yayin wata ziyara da ya kai wa abokin takararsa dake Kano, Dokta Junaidu Mohammed. Ya fadi haka ne ta bakin shugaban jam’iyyar na Jigawa, Malam Abba Anas Adamu.

Ya ce har yanzu Arewa ita ce koma baya ta fuskar tattalin arziki babu wasu abubuwan more rayuwa da aka yi wa Arewa an yi watsi da Arewacin kasar babu wani cigaba, alhali ana rawa da bazarsu ana wawashe dukiyar.

“Duba da matsayin Arewa a siyasar Najeriya, ita uwa ce wacce dole a tafi da ita, musamman bisa yanayin arzikin da yake Arewa da dimbin arzikin dan adama da muke alfahari da shi,” in ji shi.

Ya kara da da cewa ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa su ne suke zaben duk wani Shugaban Kasa, da bazarsu ake rawa, amma a yi tuwo da garinsu a hana su. “Haka ba za ta ci gaba da faruwa ba, muna gani amma ba za mu kyale ba, dole ne a samu canji, wanda zai amfani kowa da kowa a Arewacin Najeriya.”