Kungiyar Kwallon Kafa ta ’yan kasa da shekara 17 wato Golden Eaglets a shekaranjiya Laraba ta samu hayewa zuwa gasar cin Kofin Duniya na ’Yan kasa da shekara 17 da zai gudana a Brazil a bana.
Kungiyar ta samu wannan nasarar ce bayan ta doke Angola a wasanta na biyu da ci 1-0. Kuma kawo yanzu Eaglets ce ta farko a Nahiyar Afirka da ta samu nasarar hayewa zuwa gasar da za ta gudana a Brazil.
Yanzu dai Najeriya ta samu nasara a wasanni biyun da ta yi. A wasanta na farko da kasar Tanzaniya mai masaukin baki, an tashi ne da ci 5-4 inda Najeriya ta samu nasara, sai wasa na biyu inda Najeriya ta doke Angola da ci 1-0 sai kuma wasan da Najeriya za ta yi na uku a gobe Asabar a tsakaninta da kasar Uganda.
Sai dai wasan na gobe zai kasance tamkar na cika ka’ida ne don komai ya faru Najeriya ta riga ta haye gasar cin Kofin Duniyar a Brazil.
Kasashe hudun da suka kai matakin semi-fainal ne za su wakilci Afirka a gasar ta ’yan kasa da shekara 17 a Brazil a bana.