✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Edo 2020: Ba kallon gari za mu je ba– Hamza Soye

A shirye-shiryen fafatawa a gasar wasanni ta kasa a garin Benin Jihar Edo da za a fara daga ranar 22 ga Maris, Jihar Gombe ta ce…

A shirye-shiryen fafatawa a gasar wasanni ta kasa a garin Benin Jihar Edo da za a fara daga ranar 22 ga Maris, Jihar Gombe ta ce ba kallon gari za ta je jihar ba za ta je ni da niyyar samun lambobin a wasanni 14 daga cikin 31 da ta shiga.

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Gombe Malam Hamza Adamu Soye ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata lokacin da ya kira taron manema labarai kan  shirye-shiryen da suke yi a halin yanzu.

Malam Hamza Soye, ya ce duk wani shiri sun gama kan wannan gasar domin hatta bangare kula da lafiyar ’yan wasa a inda suke atisaye suna da karamin wajen kula da lafiya saboda duba ’yan wasan sannan idan suka tafi Edo za su je ne da kwararru a bangaren lafiya da suke karkashin hukumar wasanni.

Daga karshe Malam Adamu Soye, ya tabbatar wa manema labarai cewa ’yan wasan Jihar Gombe za su tafi ne da niyyar ciwo wa jihar kyaututtuka a duk  fannin wasan da suka shiga.