Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

EFCC ta kai samame gidan Abdul’aziz Yari

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Tu’annati (EFCC), ta kai wani samame gidan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar.

Bayanai sun ce kusan jami’ai 20 ne na hukumar suka isa gidan tsohon Gwamnan a garin Talata Mafara da ke jihar.

ADVERTISEMENT

Kakakin Hukumar EFCC, Tony Orilade ya tabbatar da cewa hukumar ta kai wannan samame, ya kuma ce sun yi haka ne a dalilin wani bincike da suke gudanarwa.

Ya ce, “Zan iya tabbatar muku cewa jami’anmu sun kai wannan samame zuwa gidan tsohon Gwamnan,” amma bai yi karin haske ba.

ADVERTISEMENT

Kakakin tsohon Gwamnan, Ibrahim Dosara ya tabbatar wa da gidan rediyon BBC aukuwar wannan lamarin a ranar Asabar din da ta gabata da daddare, amma ya ce jami’an na EFCC ba su dauki wani abu daga gidan ba.