✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama jami’an INEC 4 saboda karkatar da Naira Miliyan 84.7

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) reshen jihar Sakkwato ta kama jami’an Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) su 4…

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) reshen jihar Sakkwato ta kama jami’an Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) su 4 saboda zargin su da karkatar da kudaden alawun na ma’aikatan wucin gadi da kudin ya kai Naira miliyan 84.6.

Kakakin hukumar EFCC Mista Wilson Uwujaren, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a cibiyar ofishin Hukumar da ke Jihar Sakkwato a ranar Laraban nan.

A cewar Mista Wilson, hakan ya biyo bayan korafin da wani mai suna Abdullahi Nasiru, ya yi a madadin ma’aikatan wucin gadi da suka aikin babban zaben 2019 a jihar Zamfara.

Ma’aikatan dai sun ce jami’an INEC ba su biya su kudin alawus Naira dubu 6 na zirgazirga lokacin zaben ba.