✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama tsohon kansila kan zargin satar motoci

Hukumar  Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani tsohon kansila a Karamar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara Mista Samuel Opeyemi bisa…

Hukumar  Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani tsohon kansila a Karamar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara Mista Samuel Opeyemi bisa zarginsa da kasancewa jagoran gungun masu satar motoci daga hannun dillalan da suke nuna musu cewa sun je sayan mota ne.

Kakakin Hukumar  EFCC, Mista Wilson Uwajaren, ya ce hukumar ta dade tana neman tsohon kansila Samuel Opeyemi a dalilin takardun kararraki da ta rika samu daga dillalan motoci a sassan wannan shiyya.

Binciken ya nuna cewa, sau da yawa tsohon kansilan kan nuna kansa a matsayin likita ne ga dillalan motocin da yake bayar da sunayen bogi na wuraren da yake aiki da ceki na banki na bogi domin zambatarsu miliyoyin kudi. Hukumar ta ce, irin haka a baya-bayan nan ya auku sau uku a Ibadan, inda wanda ake zargin ya bayar da cekin banki mai dauke da sunan bogi na fiye da Naira miliyan hudu. Hukumar ta ce, da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da tsohon kansilan a gaban kotu domin yanke masa hukunci daidai da irin laifin da ake zargin ya aikata.