✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama ’yan damfara yahu-yahu 36

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki tu’annati ta aiwatar da wani samame, inda ta kame mutane 36 masu shekaru daga 19…

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki tu’annati ta aiwatar da wani samame, inda ta kame mutane 36 masu shekaru daga 19 zuwa 34 da ake zargin suna damfarar mutane miliyoyin kudi ta hanyar yanar gizo, wadanda aka fi sani da ’yan yahoo-yahoo.

Kwamandan Rundunar ta EFCC dake kula da Sashen Kudu maso Yamma, Alhaji Abdulrasheed Bawa shi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis ta makon jiya a lokacin da yake jagorantar manyan jami’an hukumar da suka nuna wadanda ake zargin da irin kayan da aka samu a tare da su ga manema labarai a ofishinsa dake Ibadan.

Ya ce 24 daga cikinsu dalibai ne dake karatu a Jami’ar Olabisi Onabanjo dake Ago-Iwoye a Jihar Ogun. Haka kuma kamen ya hada da wasu ’yan mata 9 wadanda makwabta ne ga daliban da suke mu’amala samari da ’yan mata.

Kayayyaki mallakar wadannan matasa ’yan yahoo-yahoo da aka baje kolinsu sun hada da kananan motocin alfarma masu tsada da dubban kudi da daruruwan katin layin wayoyin tarho da magungunan tsafi na (Babalawo) da suke amfani da su wajen damfarar mutane a kasashen duniya daban-daban.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, Kwamanda Abdulrasheed Bawa ya ce, “mun dade muna yin binciken kwakwaf a kan irin dabarun da wadannan matasa suke yi wajen yin amfani da yanar gizo (internet) suna damfarar mutane miliyoyin kudade daga kasashen duniya daban-daban. Amma sai a makon jiya ne dubunsu ya cika muka yi masu dirar mikiya a inda muka kama mutane 36 daga cikinsu.”

“A binciken da muka gudanar mun gano daya daga cikin dabarar da suke yi ita ce,  maza daga cikinsu suna samo hotunan kyawawan ‘yan mata da suke yin amfani da manhajojin Facebook da Whatsapp da makamantansu wajen tura irin wadannan hotuna ga maza masu sha’awar mata a kasashen duniya da suke turo masu miliyoyin kudi suna bushasha.”

“Daya daga cikin daliban da muka kama mun same shi dauke da katin (sim) na wayar salula guda 116 da yake yin irin damfarar shi ta hanyar dabarar rufe layukan fadebook na mutane yana sanya sabon layi da bude ajiyar bankin facebook na mutanen da yake tuntubar abokanan huldar masu layukan na hakika yana gaya masu yana bukatar kudade daga gare su.” Inji Kwamandan.

Da yake amsa wata tambaya cewa ya yi “kwarai kuwa Hukumar EFCC tana matukar bukatar taimakon ‘yan Najeriya a ko’ina suke a duniya su kawo dauki wajen bayar da bayanan sirri da zasu taimaka wajen ceto kasa daga abubuwan kunya da irin wadannan yara suke yi a kasashen waje.

“A kowane lokaci muka halarci manyan taro a kasashen duniya sai ka ji mutanen wasu kasashe suna kallonmu suna nuna mana cewa suna sane da ma’anar 419 da al’ummarmu ke yi. Saboda haka akwai bukatar janyo irin wadannan matasa ‘yan yahoo-yahoo kusa da mahukunta domin yin amfani da kwakwalwa da basirarsu da zai iya yin maganin karuwar irin wannan al’amari a nan gaba a Najeriya.”

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su ne gaban kuliya domin yanke masu hukumunci daidai da irin laifin da ake zargin sun aikata.