✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFFC ta kame wani Injiniya mai damfarar kudi ta ATM a Ilorin

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC shiyyar Ilorin, sun kama wani Injiniya mai shekaru 41, Hameed Folorunsho Lanre, bisa…

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC shiyyar Ilorin, sun kama wani Injiniya mai shekaru 41, Hameed Folorunsho Lanre, bisa zargin ya cire kudi daga asusun bankin abokinsa, ba tare da sanin abokin ba, ta hanyar amfani da na’urar cirar kudi ATM.

Rahotanni sun ce, wanda ake zargin, Hameed, da ke zama a Oke-Amun, cikin jihar Legas, ya shigo garin Ilorin ne dan ziyartar abokin nasa, mai suna Hameed Muritala, inda ya karbi lambobin sirrin ajiyar aminin nasa, sa’annan ya tura Naira dubu 540 zuwa asusunsa na cacar BetNaija.

Rigimar ta faro ne, a sa’ilin da abokin wanda ake zargin, ya rubuta koke zuwa hukumar ta EFCCn, ya na zargin an ha’ince shi ta hanyar sauya akalar wadannan kudaden daga asusun ajiyarsa a bankin Stanbic IBTC.

Hukumar a yayin bincikenta, ta gano cewa, an tura kudaden ne zuwa asusun wannan abokin nasa, mai suna Hameed.

Hukumar ta ce, ta bibiyi wanda ake zargin zuwa birnin Legas, inda ta cafke shi, kuma za a gurfanar da shi gaban kuliya, nan ba da jimawa ba.