✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya bude masallatan Juma’a

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ba da umarnin bude masallatan Juma’a da coci-coci domin a ci gaba da gudanar da ibadu bayan rufe su…

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ba da umarnin bude masallatan Juma’a da coci-coci domin a ci gaba da gudanar da ibadu bayan rufe su na tsawon watanni biyu.

An rufe wuraren ibadan ne sama da kwanaki 75 da suka wuce a yunkurin jihar na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Gwamna El’rufai ya bayyana dage dokar ne a jawabinsa ga jama’ar jihar a ranar Talata.

Ya ce daga yanzu jama’a za su rika fita daga 9:00 na safiya  zuwa 3:00 na rana kullum daga ranar Laraba 10 ga watan Yunin 2020.

Makarantu da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci, saboda har yanzu akwai hadarin kamuwa da cutar.

El-Rufai ya ce gwamnati na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar domin fito da hanyoyi da suka dace da za a dage dokar baki daya.

“Wuraren kasuwanci na iya bude su bisa sharadin za su rika amfani fa na’urar auna zafin jiki da wanke hannu da kuma da ba da tazara a tsakanin al’umma a lokutan fita daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana a kullum,” inji shi.

Ya ce “Za’a bude coci-coci ne ranakun Lahadi, masallatan Juma’a kuma a ranar Juma’a, muddin an kiyaye ka’idojin”.

Gwamnati za ta iya sake rufe wuraren matukar aka ki bin ka’idojin”, a cewar gwamnan.

Ya kara da cewa dole masu shekararu fiye 50 da haihuwa su rika taka-tsantsan saboda kauce wa kamuwa da cutar.

Sannan jamj’an tsaro za su ci gaba da ganin an bi dokar sanya takunkumi a fadin jihar.