✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya sa dokar hana fita a Kaduna

Dokar hana fitar ta fara aiki nan take a kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a kananan hukumomin Kaduna da Kudu da Chikun.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya sanar da haka ranar Asabar cewa dokar ta fara aiki ne nan take.

“An umarci jami’an tsaro da su tabbatar da dokar tare da hukunta dok wanda aka samu yana satar kaya ko lalatawa”, inji shi.

Jihar ta sanya dokar ne bayan matasa sun fasa dakun ajiyar kayan abincin tallafin COVID-19 a kananan hukumomin suna awon gaba da su.

Kwamishinan ya ce dokar hana fitar ta shafi unguwannin Barnawa, Kakuri, da Television a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.

A Chikun kuma unguwannin Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi da Ungwan Romi ta shafa.

Ya yi tir da abin da ya kira tunzura mutane da ake yi a kafafen sada zumunta inda ya roki jama’ar jihar da kar su bayar da kai bori ya hau a gurinmasu neman tayar da fitina a Jihar Kaduna.