Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

El-Rufa’i yana tsaye kan kafafunsa – APC

Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Koli ya ce ba don Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya tsaya da kafafunsa ba, da tuni wadansu sun tadiye kafafun jam’iyyar da kuma nasa ta hanyar haddasa tashe-tashen hankula domin firgita shi da tilasta biya bukatunsu na kashin kai.

Shugaban Jam’iyyar APC din ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da  Aminiya a garin Kafanchan inda ya ce da a ce Gwamnan ya fada wannan tarko kamar yadda aka jefa shugabannin jihar da suka shude da har yanzu jihar na nan kamar yadda take a baya ba tare da samun ci gaba irin wanda ake gani yanzu a fannonin kiwon lafiya da ilimi da noma da tsaro musamman a yankin Kudancin Jihar ba.

ADVERTISEMENT

“Sanin kowa ne yadda wannan sashi na Jihar Kaduna ya yi kaurin suna a baya wajen tashe-tashen hankula musamman na manoma da makiyaya inda hatta Gwamnan bai tsira ba tunda ya zo an jejjefi motarsa da na ayarinsa don a jefa masa tsoro a zuciya a kan yankin, amma da ya tsaya da kafafunsa, dubi yadda yankin yanzu ya zamo abin sha’awa ta yadda ko ka ji labarin kai hari to wadansu marasa son zaman lafiya ne kawai ke kaiwa don nuna gazawar gwamnati inda a wasu lokuta ma rikicin cikin gida ne na wata kabila sai a fake cewa ’yan bindiga da ake zaton makiyaya ne suka kai harin, amma da zarar an yi bincike sai a tarar ba su ba ne,” inji shi.

Ya bayyana cewa da a ce shugabanni za su cire tsoron wata kabila ko wani jinsi ko yanki a zukatansu su kalli kowane dan kasa a matsayin abu guda sannan su yi abin da ya fi dacewa da tuni kasar ta tsere sa’a wajen ci gaba.

ADVERTISEMENT

Da ya juya kan sabuwar Majalisar Dokoki ta Kasa ya yi kira kan su dage su bai wa marada kunya da ba sa kaunar ganin nasarar wannan gwamnati kan duk abin da ta sanya a gaba.

“Tunda Allah Ya sa dukkan shugabannin majalisun biyu na hannun damar Shugaba Buhari ne, muna yi musu kyakkyawan fata kan bai wa Shugaban Kasa goyon baya kan kyawawan manufofi da kudirorinsa na ci gaban kasa,” inji shi.