✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Mutun 69 ne suka mutu a zanga-zanga

Shugaban Buhari ya ce an kashe akalla mutum 69 a zanga-zangar #EndSARS da aka shafe akalla mako biyu ana yi a Najeriya. Buhari ya ce…

Shugaban Buhari ya ce an kashe akalla mutum 69 a zanga-zangar #EndSARS da aka shafe akalla mako biyu ana yi a Najeriya.

Buhari ya ce wadanda suka mutun sun hada da farar hula, da jami’an ‘yan sanda da sojoji.

Alkalaman da shugaban ya bayar sun haura wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar.

Amnesty ta ta ce an kusan mutane 56 ne suka mutu daga fara zanga-zangar.

A cewartsa, mamatan sun hada da masu zanga-zangar #EndSARS 12 da aka kashe a Legas ranar Talata.