Search
Subscribe
Fadar sarkin Hausawa ta tabbatar da nadin sarautu 6 a masarautar Ibadan

Fadar sarkin Hausawa ta tabbatar da nadin sarautu 6 a masarautar Ibadan

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya yi kira ga ‘yan Arewa su fiye da miliyan 10 da ke zaune a sashen Kudu maso Yammacin kasa da su tabbata sun ci gaba da bayar da gudunmawar hadin kan Najeriya da ci gabanta kamar yadda suka saba yi a baya domin samun

dunkulalliyar kasa. Ya nemi jama’a su rinka fadin gaskiyar abubuwan da suka tabbatar da aukuwarsu su daina baza jita jitar da za ta iya haifar da koma bayan ci gabansu a wannan sashe na kasa.

Sarkin Hausawan ya yi wannan kira ne a wajen bikin nada mutum 6 a matsayin hakimai kuma ’yan majalisa a masarautar Ibadan. An gudanar da bikin ne a fadar Sarkin da ke unguwar Sabo cikin birnin Ibadan.

Mutanen da Sarkin ya mika masu satifiket domin tabbatar da mukaman, sun hada da Alhaji Usman Garba Leku a matsayin sabon Magajin Garin Ibadan da Alhaji Ibrahim Haruna da aka ba shi sarautar Barden Ibadan da Alhaji Mukhatar Ali Sani a matsayin Uban Doman Ibadan. Sauran sun hada da Alhaji Mannir Mohammed da ya samu sarautar Wakilin Sarkin Samarin Ibadan da Alhaji Iliyasu Abdulmumin Gado da aka nada a matsayin Mai Unguwar Agbeni da Alhaji Isa Nalado da aka tabbatar masa da mukamin Shugaban al’ummar Hausawan Ibadan a kasuwar Sasa.

Da yake karin haske a kan rikicin nadin sarautu irin wannan, Sarkin Hausawan ya ce, “duka mutum 6 da masarautar Hausawan Ibadan ta tabbatar da nada su a yau, sun samu goyon baya ne daga jama’arsu da suka bayar da sunayensu. Ni kuma tare da ‘yan majaisa ta muka dauki dogon

lokaci muna duba cancantar nada su a kan sarautun da muka tabbatar masu a yau,” inji Sarkin.

A nan sai Sarkin ya nemi jama’a su ci gaba da bayar da muhimman shawarwari da za su kai ga cimma buri musamman hadin kan jama’ar Arewacin kasa da ke zaune a masarautar hausawan Ibadan. Ya ce, kofar fadar sa a bude take ga dukkan masu sha’awar bayar da shawara da za ta hada kan jama’a da ci gabansu. Ya yi kira gare su da su rinka girmama dokokin kasa a wuraren da suke zaune su daina yanke wa kansu hukumci a lokutan da ake samun sabani a tsakaninsu da jama’ar gari (Yarbawa).

Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Alhaji Attahiru Isa shi ne ya wakilci Kwamishinan ’yan sanda Abiodun Odude a wajen bikin. Dakta Mohammed Kola Balogun da ke son tsayawa takarar Gwamna a inuwar jam’iyar APC a Jihar Oyo yana daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin. Sababbin masu sarautun sun yi hawan dawakai da kade kade da busar Algaita da suka shere jama’a a wannan birni na Ibadan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin